1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sambo Dasuki ya gurfana a kotu

Uwais Abubakar Idris/Usman Shehu UsmanSeptember 1, 2015

A Najeriya alkali ya bada belin tsohon mai baiwa shugaba Goodluck Jonathan shawara a fanin tsaro wanda aka tuhuma da malakar manyan makamai ba bisa doka ba.

https://p.dw.com/p/1GKOb
Irak Kuwait Waffenschmuggel
Hoto: Getty Images/AFP/N. Hashem

To tunda sanyi safiya ne dai babbar kotun da ke Abuja ta cika makil inda aka fara wannan sharia wacce alkali Adeniji Ademola Ademola Adeniyi ya jagoranta, an dai karantawa kanal Sambo Dasuki laifin da ake zarghinsa da aikatawa na malakar manyan makamai da suka hada da manyan bindigogi kala biyar ba bisa doka ba, domin kuwa bashi da lasisin iznin malakarsu, laifin da ya sabawa sashin na 27 na tsarin mulkin Najeriya.


Dasuki wanda ya bayyana a kotun ya musanta aikata laifin, kuma nan take lauyoyinsa suka nemi da a bada belinsa, abinda lauyoyin da ke tuhuma suka ce basu da ja, sun barwa kotu ikon yanke hukunce a kan lafin. Alkalin kotun Adeniyi Ademola dai ya amince da bada belin Kanal Sambo Dasuki bisa matsayinsa a kasa ba tare da wata ja in ja ba. To ko wadanne hujjoji suka bayar kotun ta amince da bada belin? Mr Joseph Daudu shi ne lauyan da ke kare Dasuki.


‘’Dama tsarin mulki ya bada hurumi a bashi beli, domin a tsarin mulki wanda ake tuhuma ai baya da laifi don haka dole ne a bashi belinsa, tunda yana matsayin wanda ake tuhuma har yanzu, shi yasa alkali ya amince da hakan’’.
Lauyan gwamnatin Najeriya da ke jagorantar jerin lauyoyin masu tuhumar wanda ake zargi Barrister Mohammed Diri yaki cewa uffan, a kan wannan shari’a da ake sa idanu a kanta sosai don ganin yadda zata kaya.


To sai dai irin yadda duka lauyoyin da ke tuhumar mai laifi da masu kare shi basu yi wata jayayya ba a kan batun bada belin da ya sanya mai sharei’a Adeniyi sake tambayar lauyoyin gwamnati bada belin, hakan ya sanya tambayar lauya Joseph Daudu ko dai dama can sun hada baki ne tun kafin su bayyana a kotu?
‘’Bamu hadu ba, ba dalili dai tunda aka bamu takardar tuhuma mun duba ta sosai bamu jira ba tare da bata lokaci ba muka shigar da wannan. Idan da da ne wasu lauyoyi ba za su yi wannan ba, sai a zaman kotun nan to shi sai ya je ya karanta. Amma mu mun riga mun yi wannan kuma ya karanta duka ya gamsu’’


Kotu dai ta umurci Kanal Sambo Dasuki da ya mika dukkanin Fasfo na tafiye-tafiyensa ga kotun da ma sauran takardu, kafin a bada ikon bashi beli.
Tuni dai jami’an tsohuwar gwamnatin ke karaji tuhumar da ake yi masu ta zargin aikata ba dai dai ba, amma a wata zantawar da na yi da shi jigo a jamiyyar da ke mulki Sanata Hadi Sirika bayyana cewa.


‘’Kasar nan an taho ganrara an yi abinda aka ga dama an yi galatsi kala-kala an zalunci al’umma, saboda me yasa Muhammadu Buhari wanda al’umma suka nada mashi "Mai gaskiya" ace ya ci mulki ya kasa wannan, me za’a ciza me za’a hura, wannan in ya magana ce kawai’’


Wannan shari’a ta tuhumar da ake yi wa kanal Sambo Dasuki mai ritaya dai, ta kasance mai daukan hankali sosai a cikin kasar . Saboda ita ce ta farko a jerin shari’o'in da ake sa ran yi a kan tuhumar aikata ba dai-dai ba ga jami’an tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan. Mai shari’a ya tsayar da ranar 27 ga watan Octoban nan domin ci gaba da shari’ar.