1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Samar da mafita a rikicin Ukraine

February 6, 2015

Shugabar gwamnatin Angela Merkel da Francois Hollande na ƙasar Faransa sun ƙaddamar da wani sabon shiri kan ƙasar Ukraine bayan wani zaman ganawa a birnin Kiev na ƙasar Ukraine a jiya Alhamis.

https://p.dw.com/p/1EWMh
Ukraine Kiew Merkel Poroschenko Hollande
Hoto: S. Supinsky/AFP/Getty Images

Shugabannin biyu kuma a yau Jumma'a su ke shirin yin wata ganawar da shugaba Vladimir Putin na ƙasar Rasha.

Shugaba Hollande ya faɗa wa taron manema labarai cewar cikin batutuwan da za a maida hankali cikin sabuwar buƙatar da ake son gabatarwa sun haɗa da samar da mafita ga kutsen da ake wa kan iyakokin ƙasar ta Ukraine.

A cewar wakilin DW a birnin Kiev Frank Hofmann ɗaya daga cikin manyan abubuwa da ake gani yanzu na zama yadda 'yan tawayen ke kara mamayar yankuna. Cikin makon da ya gabata ɓangaren na 'yan tawaye ya samu damar sake mamayar kimanin murabba'in kilomita 500 tun daga tsakiyar watan Janairu.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Abdourahamane Hassane