Samar da ilimi da jari ga nakasassu a Kano | Sauyi a Afirka | DW | 09.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Sauyi a Afirka

Samar da ilimi da jari ga nakasassu a Kano

Wani matashi a Kano wanda ya sami nakasar hannuwa da kafafu mai suna Abba Sarki ya himmatu wajen dogaro da kai har ma da taimaka wa wasu yaran masu larurar nakasa samun cigaba a fannin Ilmi.

Behinderte in Arika - Rollstuhlfahrer (picture-alliance / dpa)

 

Wani matashi a Kano wanda ya sami nakasar hannuwa da kafafu ya himmatu wajen dogaro da kai har ma da taimaka wa wasu yaran masu larurar nakasa samun cigaba wajen sha'anin ilmi ta hanyar kungiyar da ya kafa da ke fafutukar ganin cigaban nakasassu.

 

Abba Sarki Daneji matashi ne wanda Allah ya jarrabe shi da lalurar shanyewar hannuwa da kafafu tun yana kankani, a firar da ya yi da DW ya ce wannan matsalar ce ta hanashi cigaba da karatu har wannan lokaci. Dalilin haka ne ma ya kafa wata kungiya mai fafutukar kare hakkin nakasassu da kuma sama musu guraben karatu a makarantu masu zaman kansu, ba tare da sun biya kudi ba. Kuma a yanzu kungiyar tasu ta mika wani kudirin doka da zai magance nunawa dalibai masu nakasa wariya musamman a makarantu.

 

Sarki Abba Sharada ya hadu da lalurar nakasa a sakamakon gwajin allurar Trovan da wani kamfanin Amirka ya yi a kan wasu yara a Kano shekaru sama da 20 da suka gabata. Wannan matsala ce ta kassara masa damar cigaba da karatu tun daga matakin Primary, Abba sarki ya zama koyaushe yana kan kujerar guragu ana tura shi, kuma a cewarsa takaicin rashin damar ci gaba da karatu da kuma irin wariyar da masu nakasa irinsa ke fuskanta sune suka yi masa kaimi wajen kafa wannan kungiya.

To ko wadanne irin ayyuka wannan kungiya wacce ake wa lakabi da kungiyar kare hakkin nakasasu ta Kanawa ke yi? Abba sarki ya yi mana karin haske:

 

"Duba da irin matsalolin da masu nakasa ke samu wajen ilimi da sana'a wanda ke tilasta musu yin bara ya sa muka fito da wani tsari na samar musu guraben karatu a makarantu masu zaman kansu, kuma kungiyarmu kan samar musu da littattafai da sauran kayan makaranta. Haka kuma mukan koya masu sana'o'i da basu jari domin su dogara da kansu su kauce wa bara"

 

Yanzu haka wannan kungiya ta gabatar wa da majalisar dokokin jihar Kano wani kudiri da zai bai wa nakasassu 'yanci musamman a wajen karatu kamar yadda Abba sarkin ya yi mana karin haske:

 

"Akwai makarantun da ke nuna wa nakasassu wariya haka ma a fannonin rayuwa nakasassu kan fuskanci tsangwama, dan haka muka mika wannan kudiri na nema wa nakasassu 'yanci tun da mutane ne kamar kowa".

Poliobekämpfung Nordnigeria (Thomas Kruchem)

 

Nakasassu da dama ne suka amfana da ayyukan wannan kungiya har ma DW ta zanta da wasu yara da ke makarantun primary daban-daban a Kano wadanda suka ce wannan kungiya ce ta saka su. Sun bayyana cewar sun sami labarin kungiyar ne ta kafar yada labarai kuma sun je sun sami takardar izinin shiga makaranta, har ma sun fara karatu a matakai daban-daban .

Yanzu haka dai Sarki Abba ya koka bisa dimbin kalubale da ke gaban wannan kungiya, ya ce duk da cewar sun yaye matasa dama nakasassu amma karancin kudi da karancin kulawa daga sauran masu rike da madafun iko na daga cikin abin da ke ciwa kungiyar tuwo a kwarya.