Samar da aiki ga matasa aiki a Bauchi | Sauyi a Afirka | DW | 13.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Sauyi a Afirka

Samar da aiki ga matasa aiki a Bauchi

Wani dan siyasa a Bauchi ya dukufa wajen samawa matasa aiki maimakon barinsu suna gararamba a kan tituna ko kuma wasu 'yan siyasar su yi amfani da su wajen bangar siyasa.

Dan siyasar mai suna Ali Wakili wanda ke wakiltar kudancin jihar a majalisar dattawan Najeriya ya ce ya dauki aniyar samawa matasan sana'o'i ne maimakon a kyalesu suna zaman kashe wando kuma ya na amfani da irin kudaden da ake basu wajen yin aiyyukan mazabu wajen yin wannan yunkuri.

Matasa dama da dari ne dai suka amfana da wannan shiri wanda ya hada da koya musu sana'ar daukar hoto na bidiyo da aiki da kwamfiyuta wajen tace hotunan yayin da wasunsu suka koyi sana'ar walda. Baya ga koyawa matasan sana'a, dan majalisar har wa yau ya basu kayan da za su yi aiki da su. Jama'a a jihar sun jinjinawa wannan kokari inda suka ce hakan zai taimaka wajen bunkasar tattalin arziki da kuma magance tashin hankali da matasa marasa aikin yi kan haifar.