Samamen kakkabe 'yan tarzoma a Jamus
June 23, 2017Talla
Dama dai jami'an tsaro sun dira ne a jihar Thuringen da ke gabashin kasar kasar ta Jamus, don murgushe wasu gungun masu tsattsauran ra'ayi da ke da sansanin horas da magoya bayansu. Kungiyar masu kyamar baki ne dai sukan kai farmaki kan 'yan sanda, da baki masu neman mafaka kana da Yahudawa. Samamen da aka kai a yau Juma'a, ya samu hadin gwiwar 'yan sandan jiha da na tarayya, a wani kokarin da hukumomi ke yi na kakkabe irin wadannan kungiyoyi.