Sama da mutane 140 sun bace a Bahar Rum | Labarai | DW | 29.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sama da mutane 140 sun bace a Bahar Rum

Jirgin dai da ya dauko bakin hauren ana ra san ya taso ne a ranar Litinin daga Sabratha Arewa maso Yammaci na Libiya kafin ya kife a tsakiyar teku.

Kimanin bakin haure 146 ne ake da fargabar sun bace bayan da jirgin da ya dauko su ya kife bayan baro gabar teku a Libiya kamar yadda wani dan kasar Gambiya da aka ceto shi cikin mutanen ya fada wa cibiyar Majalisar Dinkin Duniya da ke lura da 'yan gudun hijira a ranar Laraba.

Jirgin da ya dauko bakin hauren ana ra san ya taso ne a ranar Litinin daga Sabratha Arewa maso Yammaci na Libiya ,kuma cikin jirgin akwai mata masu ciki da yara kamar yadda dan kasar ta Gambiya ya fadawa hukumar ta MDD a wani asibiti da ke a Lampedus.a

Ya ce mafi yawa na fasinjojin jirgin sun fito ne daga kasashen Najeriya da Mali da Gambiya. A cewar cibiyar da ke kula da 'yan gudun hijira ta kasa da kasa (IOM) bakin haure 590 ne suka rasu ko suka bace bayan baro gabar tekun a Libiya sakamakon kifewar jirginsu.