1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saliyo: An jinkirta fadin sakamakon zabe

Abdullahi Tanko Bala
April 3, 2018

An sami tsaiko a kidayar kuri'un da aka kada na zaben shugaban kasa a Saliyo, lamarin kuma da ya jawo jinkiri wajen sakamakon zaben.

https://p.dw.com/p/2vOFj
Sierra Leone Wahlen 2007
Hoto: Getty Images/AFP

Hukumar zaben kasar Saliyo ta sanar da jinkirta baiyana sakamakon zaben shugaban kasar zuwa ranar Alhamis saboda rashin jituwar da aka samu game da matakan da ake bi na kidayar kuri'un.

Tun da farko dai an shirya sanar da sakamakon zaben na ranar 31 ga watan Maris ne wanda aka yi karan batta tsakanin madugun adawa Julius Maada Bio da kuma dan takarar jam'iyyar APC mai mulki Samura Kamara a farkon wannan makon.

Hukumar zaben ta ce bayan tattaunawa tsakanin wakilan yan takarar an cimma daidaito kuma an ci gaba da kidayar kuri'un.