Salam Fayyad : saban Praministan Palestinu
June 15, 2007Talla
Shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, ya naɗa Salam Fayyad, a matsayin saban Praminsitan riƙwan ƙwarya, wanda zai cenji Isma´il Hanniey.
Jine ne fadar shugaban ƙasar, ta bayyana rusa gwamnatin haɗin kan ƙasa, da Hanniey ke jagoranta, tare kuma da kafa dokar ta ɓace,a matsayin martani ga tashe-tashen hankulla da ke wakana a zirin Gaza.
To saidai Isma´il Hanniey, ya bayyana ƙin amincewa da matakin rusa gwamnati.
Salam Fayyad, tsofan jami´in assusun bada lamani na dunia, ya samu cikkaken haɗin kai, daga ƙasashen yammacin dunia.
A russasar gwamnatin, shike riƙe da matsayin ministan kuɗi.
Ya na jagorantar wata ƙaramar jam´iya, wadda ba ta da alaƙa da Hamas, da kuma Fatah.