1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakon bam ga Angela Merkel

Usman ShehuNovember 2, 2010

jami'an 'yan sandan Jamus sun bankado sakon bam da aka aikawa shugabar gwamnati Angela Merkel.

https://p.dw.com/p/Pwk2
Angela MerkelHoto: AP

Jami'an da ke kula da tsaron shugabar gwamantin Jamus sun duƙufa domin tantance ko saƙon da aka aka aiko wa Angela Merkel na ɗauke da bam, koko a'a. Fadar mulki ta Berlin ta bankaɗo wani saƙo da ake kyatata zato ya taso ne daga ƙasar Girka da kuma ke ƙunshe da bam. Ita dai Merkel da ke zama shugaba ta biyu a nahiyar Turai da aka aika wa makamacin wannan saƙo, ta fara ziyarar aiki a ƙasar Beljium.

A ɗaya hannun kuma Wasu ƙananan bama-bamai biyar sun fashe a ofishin jakadancin Rasha da ke Athenes, sa'o'i ƙalilan bayan tarwatsewar wani bam a ofishin jakadacin Switzerland da ke babban birnin ƙasar ta Girka. Jami'an 'yan sandan ƙasar sun kuma yi nasarar bankado sakwanin da ke kunshe da bama-bamai da aka tura ofisoshin jakadancin Chili da Jamus da kuma Bulgariya.

Hukumomin Athenes na ɗora alhakin wannan yunƙurin ƙaddamar da hare-haren ƙunar baƙin wake kan ƙungiyoyin da ke da tsattsaruran ra'ayi. Ya zuwa yanzu dai 'yan sanda sun yi nasarar tsare matasa biyu da shekarunsu na haihuwa bai tasamma 25 ba bisa laifin samunsu da nakiyoyi a birnin Athenes. A jimilce dai, bama-bamai tara aka yi nasarar ganowa tun bayan bankaɗo hare-haren ƙunar baƙin waken na ƙasar ta Girka.n

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Ahmed Tijjani Lawal