Sako-sako da hukuncin adalci a Afirka | Siyasa | DW | 24.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sako-sako da hukuncin adalci a Afirka

Ana ci gaba da famar kai ruwa rana game da hukunta gaggan masu alhakin kashe-kashen ƙare dangi a Afirka

default

Tsofon shugaban Liberiya Charles Taylor gaban kotun ƙasa da ƙasa a The Hague ta Netherlands

Har dai ya zuwa halin da muke ciki yanzun akwai ɗaruruwan masu alhakin laifukan kashe-kashen gillar da suka wakana a Kenya, Darfur, Kongo da arewacin Uganda, waɗanda kawo yanzu ba a gurfanar da su gaban kuliya ba, ballantana ma a yi batu game da biyan diyya ga waɗanda wannan ɗanyyen aiki ya shafa. Kotun ƙasa da ƙasa na ci gaba da famar ganin an kawo ƙarshen wannan sako-sako da ake yi da maganar shari'ar. To sai dai kuma maƙurar ƙoƙarin nata ta fito fili a birnin Berlin wannan makon. A ƙarƙashin taken:"Duk wani abin da ya danganci adalci" masu alƙalai da masu fafutukar kare haƙƙin ɗan-Adam suka tattatauna matsalar adalci a wannan duniyar dake daɗa zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya. An saurara daga Fatou Besounda tana mai bayanin cewar:

"Za mu gurfanar da Thomas Lubanga  a gaban kotu bisa laifin tilasata wa ƙananan yara shiga aikin soja. Za mu kuma hukunta Germaine Katanga da sauran waɗanda suka aikata laifukan yaƙi a ƙasashensu cikinsu har da Shugaba Omar Hassan Albashir

Fatou Besounda dai ita ce  wakiliyar shugbar kotun hukunta laifukan yaƙi a birnin the Hague na ƙasar kuma ta fito ta bayyyana sunayen waɗanda suka yi ƙaurin suna wajen cin zarafin Bil adama a nahiyar Afirka. A haƙiƙa ta na alfahari da aikinta tana kuma da imanin cewa wannan aiki nata zai yi tasiri.

Tun sanda kotun hukunta miyagun laifuka ta ƙasa da ƙasa dake birnin the Hague ta ba da sammace akan shugaba Umar Hassan Al_bashir na ƙasar Sudan ne dai aka fara shigar da ƙara game da mutanen da suka yi ƙaurin suna wajen aikata ta'asa. Kai Ambos jami'in kare haƙƙin jama'a ne a kotun . Yana mai ra'ayin cewa tsai da adalcin shari'a shi ne hukunta mutun ba  tare da yin la'akari da muƙamin da ya riƙa a baya ba. Ambos ya ƙara da cewa:

"Ko shakka babu maganar Albashir ta kawo rarrabuwar kawuna a Afirka : Mun samu canjin matsayi a lokacin da aka ba da sammace akan Albashir . Ayar tambaya anan ita ce shin zamu iya hukunta shi a matsayinsa na shugaban kasa?"

A matsayin mataki na nuna danƙon zumunci ga Albashir  ƙungiyar Gamayyar Afirka ta nuna  masa goyon baya ta ƙin biye wa wannan sammacen. Ambos dai yayi imanin cewa ƙungiyar za ta ci gaba  da yin haka a duk sanda kotun ta ba da sammace akan wani shugaba na Afirka. A saboda haka ne ma  Shugaban na Sudan ya kammala ziyara da ya kai a ƙasar Kenya a baya bayan nan  gabanshi gaɗi ba tare da fuskantar wata tsangwama ba, ko da yake ƙasar ta Kenya na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka rattaba hannu akan dokar kafa kotun ta birnin the Hague.

"Wannan dai abu ne mawuyacin gaske. inji Beuthel Kiplagat jamiin kasar Kenya  kuma dan fafutukar aiwatar da zaman lafiya." Kipalagat ya ƙara da cewa:

Ni dai ba na tausaya wa Albashir game da cafke shi da ake neman yi . To amma mutun ba zai musunta cewa siyasa tana da rawar da zata taka wajen murƙushe wannan yunƙuri ba. A ganina kamun Albashir wani abu ne da ka iya dagula lamari tare da janyo ruɗani da rikici da zai yi sanadiyar asarar rauka da dama.

To sai da akasarin masu fafutukar kare  haƙƙin bil Adama na dasa ayar tambaya game da ko shin wannan adalci ne da aka tsayar ba tare da yin la'akari da cin zarafin alumma ba.Hartwig Fischer jami'in jamiyar CDU CSU ta nan Jamus, wanda ƙwararren masani ne akan alamuran Afirka ya yi kashedi da cewa  duk wani yunƙuri na diplomasiya zai ci tura.

"Shin adalci a ce an gurfanar da talaka a gaban kotu bisa laifin aikata kisa ba tare da cewa a hukunta shugaban da ya aikata irin wannan laifi ba? In har muka yi haka to kenan mun take haƙƙin alummomin da hakan ta shafa. Mun kuma ba da ƙwarin gwiwa ga masu mulkin kama karya a daidai lokacin da muke hanƙoron tabbatar da adalci a duniya."

Masana aikin sharia na ci gaba da sa ayar tambaya game da matakan da gamayyar kasa da kasa za su dauka domin  tabbatar adaclin sharia . Kipalagat  yace wajibi ne a ci gaba da nuna adalci bayan aukar yaki fiye da ma hukunta wadanda ke da laifi.

Ya ƙara da cewa  a ƙasar Ruanda akwai kotunan gargajiya irinsu ta garin Gacaca  ko kuma kwamishan tabbatar da adalci irinta Kenya da suka taka rawar gani  wajen ba kowa haƙƙinsa.

Mawallafi: Halima Balaraba Abbas

Edita: Ahmad Tijani Lawal