Sako Saddam itace hanya ta kawo karshen tashe tashen hankula a Iraq.... | Labarai | DW | 29.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sako Saddam itace hanya ta kawo karshen tashe tashen hankula a Iraq....

Shugaban tawagar lauyoyi dake kare tsohon shugaban kasar Iraqi a gaban kuliya, wato Khalil Dulaimi ya bukaci shugaba Bush na Amurka daya bada umarnin sako Saddam Hussain.

Yin hakan a cewar babban lauyan itace hanya daya da zata kawo zamman lafiya a fadin kasar ta Iraqi baki daya.

Khalil Dulaimi, wanda ya fadi hakan a cikin wata takarda daya aikewa shugaban na Amurka a yau Alhamis, ya kara da cewa kamata yayi shugaba Bush ya kyale yan iraqi suyi tunanin makomar shugaban nasu.

Har ilya yau babban lauyan ya tabbatar da cewa, matukar ba wannan mataki aka dauka, to babu shakka kasar ta iraqi ka iya fuskantar yake yake na basasa, wanda hakan a cewar sa ka iya jefa yankin gabas ta tsakiya a cikin wani hali na tsaka mai wuya.

A yanzu haka dai Saddam Hussain da mukarraban sa guda 7 na fuskantar tuhuma ne na kisan kiyashi daya wanzu a yankin Dujail a lokacin mulkin tsohon shugaban na iraqi, samun sa da wannan laifi kuma ka iya kaiwa ga yanke musu hukuncin kisa.