Sakin Vanunu daga gidan yarin Israela. | Siyasa | DW | 21.04.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakin Vanunu daga gidan yarin Israela.

Yau ne Vanunu ya samu yanci kai ,bayan kasancewa a tsare na shekaru 18.

Vanunu bayan samun yanci.

Vanunu bayan samun yanci.

Bayan kasancewa a tsare a kurkukun Izraela na tsawon shekaru 18,Mordechai vanunu,sanye da riga mai ratsi da madaurin wuya,ya fito kaitsaye tare da daga hannu domin nuna alamun nasara,wa daruruwan magoya bayansa da sukayi cincirindo a kofar Yarin Shikma dake garin Ashkelon.

A harabar wurin,Vanunu mai shgekaru 50 da haihuwa,nan take yayi taron manema labaru,tare da Danuwansa Meir,daya kasance a gefensa.Ya fadawa yan jarida cewa baya nadaman abunda yayi,a maimakon haka yana mai afahari da bayyawa wa duni sirrin mallakan makaman Nuclear na Bani Izraelan.Sai dai yaki amsa tambayoyi dangane da Hebrew,saboda dokokin da Izraelan ta gindaya masa,wadanda suka hada da haramta masa magana da Baki.

Vanunu wanda ya bar addinin Yahudanci zuwa Christa a shekarun 1980,yace an gana masa wannan azaba ne saboda sauya addini da yayi.Ya kuma kara dacewa bai halalta Bani Izraelan ta samu kasar kanta ba,tare da kira a gareta data amincewa jamian binciken majalisar dunkin duniya su ziyarci cibiyar sarrafa makamanta na nuclear dake Dimona.Vanunu yace Izraelan bata da hgujjan mallakan makaman kare dangi,musamman a yanzu da dukkan kasashen yankin gabas ta tsakiya basu da sauran makamai.

Wuri na farko daya yada zango bayan samun yancin nasa dai shine,St.george Anglican dake birnin Kudus,inda ya samu rakiyan motoci da babura masu yawan gaske,baya ga jirgi mai saukan ungulu dake rufa musu basya ta sararin samaniya.Daga cikin wadanda suka marabceshi har Peter Hounam,Dan jaridan daya rubuta labarin daya jagoranci kame Vanunu a shekarata 1986.

A shekarata 1986,Vanunu ya bayyana sirrin da hotunan makamai miyagu na kare dangi da Izraela ta mallaka wa mujallar Sunday Times ta London.A dangane da bayan nasa ne kwararru suka sanya izraelan a matsayi na 6 a jerin kasashe dake da makaman kare dangi,wanda ya jefa ta cikin halin kakanikayi,tunda daman bata amince tana dasu ba.Bayan nan ne jamian leken asirin Izraelan suka sace Vanunu,kafin a gurfanar dashi gaban kotun sirri,inda aka yanke masa hukuncin cin amanar kasa.

Yadai yi fatan ficewa daga yankin na Izraela,zuwa kasashen ketare dayake da abokanai,amma Izraelan ta haramta masa zuwa ko kusa da kann iyakar kasar balle ficewa.A yanzu haka dai Vanunu zai kasance a wani katafaren gida dake Jeffa ,a kudancin Tel Aviv.