1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakin Sojin Britania 15

April 5, 2007
https://p.dw.com/p/BuOF

Jamian Sojin ruwa na Britania dake tsare a Iran na tsawon kusan makonni biyu,sun isa birnin London yau da rana.Tun a jiya nedai shugaba Mahmoud Ahmadinejad na Iran ya sanar da yiwa jamian afuwa,tare da sakinsu a matsayin wata kyautace wa alummomin Britania.Shi kuwa a nashi bangare prime ministan Britania Tony Blair yayi maraba da sakin wadannan jamian,wanda ya dangana da tallafin mdd da sauran shugabanni na kasashen turai.

Shi kuwa ministan harkokin ketare na na nan jamus Frank-Walter Steinmeier,fata yayi nacewa warware wannan takaddama da kasar Iran,ya zamanto wata alama ce na warware sauran matsaloli mai sarkakkiya da suka hadar da shirin Nuclearnta.