Sakin Brigitte Mahnhaupt bayan shekaru 24 a gidan kurkuku | Labarai | DW | 13.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakin Brigitte Mahnhaupt bayan shekaru 24 a gidan kurkuku

Ministar kula da harkokin sharia Brigitte Zypries ya kare hukuncin da kotun ta zartar a dangane da sakin Brigitte Mohnhaupt,dake kasancewa tsohuwar wakiliyar kungiyar yan adawa na Red Army dake nan jamus ,kungiyar da akafi sani da suna Baader-Meinhof Group.Mai shekaru 57 da haihuwa,an cafke Brigitte Mohnhaupt ne a shekara ta 1982,inda aka yanke mata hukuncin daurin rai da rai a gidan yari,bayan samunta da laifin kisan gilla a matakai guda 9.A karshen watan maris mai kamawa ne zaa sake ta ,bayan kasancewa a gidan kurkuku na tsawon shekaru 24 da suka gabata.Ministar sharia ta jamus wadda ta fito daga jammiyyar SPD,da bayyana cewa wannan zartarwa na kotu yana bisa kaida.Kungiyar yan tawayen dai tayi fice ne a shekarun 1970s,wadda take da alhakin kisan gillan mutane 34.