1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakin al-Megrahi daga kurkukun Scottland

August 24, 2009

Sakin ɗan ƙasar Libya da aka ɗaure a Scottland akan laifin tarwatsa jirgin saman Amirka na kamfanin PAN AM ya fi ɗaukar hankalin jaridun

https://p.dw.com/p/JH7t
Abdel Baset al-Megrahi a hagu da ɗan shugaban Libya, Seif al-Islam Gadhafi, a dama, lokacin daya sauka Tripoli, Libya.Hoto: AP

A wannan makon mai ƙarewa jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne akan afuwar da aka yiwa ɗan ƙasar Libya nan Abdel Basit Mohammad al-Megrahi. A rahoton da ta rubuta jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta fara ne da cewa an saki mutumin da aka same shi da laifin tarwatsa wani jirgin saman Amirka a yankin Lockerbie na Scottland bayan ya shafe shekaru 10 a wani gidan yarin Scottland. Ta ce a ranar Alhamis da yamma al-Megrahi tsohon jami´in leƙen asirin Libya ya isa gida bayan sakinsa na gaba da wa´adi daga kurkuku saboda dalilai na jin ƙai. To sai dai jaridar ta ce wataƙila batun na Lockerbie ba zai taɓa ƙarewa ba.

Libyen Großbritannien Lockerbie Attentäter Ankunft in Tripolis
Hoto: AP

Scottland ta saki al-Megrahi saboda kwaɗayin man fetir ɗin Libya. Wannan shine taken sharhi da jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta kan wannan batu tana mai nuni da wata manufa ta siyasa da ta janyo sakin wannan mutumin. Ta ce yanzu da albarkatun iskar gas a Scottland na dab da ƙarewa yayin da a Libya yanzu aka gano wasu sabbin rijiyoyi mai da na gas. A saboda haka ba a buƙatar wata masaniya kafin a san cewa da walakin batun yafiyar da aka yiwa Abdel-basit ali al-Megrahi. Ta ce ba batun yafiya ko ramuwar gayya ba ne, kawai magana ce ta zuba jari na dubban miliyoyin dala ne a fannin makamashi. Jaridar ta ƙara da cewa Amirka ta yi suka ga wannan mataki ne don daɗaɗawa iyalan Amirkawan da lamarin na Lockerbie ya rutsa da su, domin gwamnatin Washington tuni ta san da batun sakin al-Megrahi. Ta ce Amirka da ta ɗauki irin wannan mataki inda a ƙasar ta aka ɗaure al-Megrahi.

Süsafrika Jacob Zuma nach der Wahl
Shugaban Afirka Ta Kudu Jacob ZumaHoto: AP

Gwamnatin Jacob Zuma na samun ci-gaba duk da matsaloli massu tarin yawa a Afirka ta Kudu, inji jaridar Neues Deutschland tana mai mayar da hankali kan halin da ake ciki a ƙasar Afirka ta Kudu kwanaki 100 bayan kama ragamar mulki da Jacob Zuma yayi. Ta ce shugaban na taka rawar ganin musamman idan aka yi la´akari da taƙaddamar da aka ta yi kansa gabanin hawarsa kan mulki. Jaridar ta ce kyakkyawan sauyin da aka samu kan yadda kafofin yaɗa labaru da kuma ´yan siyasa ke kallon Zuma ɗaya daga cikin nasarori ne ga shugaban. Duk da haka matsalolin da ƙasar ke fuskanta musamman na talauci da koma baya a harkokin kiwon lafiya da ilimi da rashin aikin yi da kuma cin hanci da rashawa suna nan ba a warware su ba. To sai dai jaridar ta ce bai kamata a yi riga malam masallaci ba wajen auna alƙawuran da Zuma yayi na samar da kyakkyawan shugabanci da kuma ingantattun hukumomin gwamnati.