1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sake masu kai agaji i zuwa zirin Gaza

June 2, 2010

Isra'ila ta yi alƙawarin sake ɗaukacin jami'an agaji da ta kama a kusa da zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/NfoJ
Hoto: AP


Isra'ila ta bayyana aniyarta na sako ɗaukacin 'yan ƙasashe waje da ta kama lokacin da ta kai farmaki kan ayarin jiragen ruwa da ke kai kayan agaji i zuwa zirin gaza. Ya zuwa yanzu dai jami'an agaji 200 ne ƙasar ta Yahudu ta yi jigilar su- daga gidan yarin Tel Aviv i zuwa filin jirgin saman wannan birni. Wasu ƙarin jami'ai 123 kuma sun rigaya sun tsallake iyakar ƙasar ta Isra'ila da kuma Jordan.

Bisa matsin lambar ƙasashen duniya ne dai -fadar mulki ta Tel Aviv ta yanke shawarar sake  ilahirin mutane 682 da suka fito daga ƙasashe 25 da ta tsare. Tuni dai Turkiya ta fara duba yiwuwar kyatata dangantarka da Isra'ila bayan mutunta kiraye kirayen ƙasashen duniya da ta ke yi.

Kwamitin sulhu na majalisar Ɗinkin duniya ya nemi sda  a gudanar da binciken domin gano gaskiyar abin da ya faru lokacin da sojojin ƙundun balar Isra'ila suka kai farmaki. Mutane tara ne dai suka rasa rayukansu a dirar miƙewan Isra'ila da duniya ta yi Allah wadai da ita.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu