SAKE GININ CONGO BAYAN YAKIN SHEKARU 10....... | Siyasa | DW | 22.12.2003
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

SAKE GININ CONGO BAYAN YAKIN SHEKARU 10.......

ZAINAB AM ABUBAKAR

Tsibirin Fizi dake gabashin Congo,yanki ne daya fuskanci matsaloli na fadace fadace a hannun yan tawayen wannan kasa,wanda a sakamakon hakane aka yanke tsibirin daga sauran harkokin na Congon.A yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a watan Yuli ne aka samu hade kann yan tawayen kasar wuri daya inda aka basu madafan iko cikin tafiyar da gwamnatin hadin kann kasa baki daya.
To sai dai a wannan yanayi da ake ciki shugabannin gudanar da gwamnatin na janhuriyar democradiyyar congo na fuskantar matsaloli na sake ginin wannan kasa bayan yakin basasa shekaru biyar daya haddsa asaran rayukan mutane million 3 a dangane da yunwa da cututtuka.Bugu da kari Tsirin Fizi na daya daga yankunan da mayakan suka mamaye,wanda yake gabashin wannan kasa.
Jamian majalisar dunkin duniya na cigaba da aki agaji zuwa kauyuka da wannan rikici ya ritsa dasu,wadanda akasarinsu basu da kayayyaki na more rayuwa,banda matsalar yunwa da kuma cututtuka babu magani.Jamiin hukumar agajin abinci na MDd Ndeley Agbaw yace bayan sun tsira daga rikicin yaki na yan tawaye,mutane a sassa daban daban na Congon na cikin hali matsananci na yunwa saboda karancin abinci.yace ya zamanto wajibi a taimakawa mutanen Congo da abinci,kafin su samu sukunin komawa gonakinsu.Yace har yanzu akwai matsaloli na sace sacen abinci da mayakan dake cikin cikin tsaunuka keyi sakamakon yunwa.
Alokacin fadace fadacen dai tsibirin Fizi ya kasance wurin mabuyan yantawayen saboda kasancewarsa a kudancin Kivu,ga kuma tsaunuka masu duhu daka yammacin tabkin Tanganyika.Yan tawayen Rwanda ne suka rike akasarin yankintare da yan tawayen Congo da suke marawa baya,watau RCD,kungiyar yan tawayen da ahalin yanzu ta hade cikin gudanar da mulkin wannan kasa,nan da shekaru biyu,lokacin da ake saran gudanar da zaben kasa baki daya.Wannan Yanki dai na karancin kayayyakin koyarwa a makaranta,ayayinda baban asibitin dake jinyan mutane dubu 300 na fuskantar karancin maaikata da magunguna,ayayinda sama da kashi daya daga cikin uku na mutane sun tsere zuwa Tanzania.Yara kanana da mata sun fuskanci mawuyaci yanayi alokacin wannan fadan.wata kungiyar mata dake Congo ta ruwaito cewa akalla mata 450 akayiwa Fyade tsakanin watannin Afrilu zuwa Satumban wannan shekaran kadai. AS shekarata 1998 yakin janhuriyar congon ya barke,alokacinda Rwanda suka mamaye kasar a kokarinsu na neman wadanda sukayi kisan kiyashin shekarata 1994.Wannan fadan dai ya lalata tattalin arzikin Congo saboda rauni da albarkatuntana luu luu da katako,ayayinda Zimbabwe da Angola suka marawa Kinsasha baya adangane da kungiyoyin yan tawayen dake da goyon bayan Rwanda da Uganda.A yanzu haka dai ana cigaba da fuskantar matsaloli wanda kuma zai kasance babban batu na yadda zaa sake gini tare da farfado da wannan kasa.