Sake fasalin manufar ƙetare na EU | Labarai | DW | 22.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sake fasalin manufar ƙetare na EU

Ƙungiyar tarayyar Turai za ta sake nazarin yadda take tinkarar lamuran ƙasa da ƙasa

default

Majalisar dokokin tarayyar turai ta ƙulla wata yarjejeniya tare da kantomar kula da harkokin ƙetare ta ƙungiyar Catherin Ashton, da nufin kaiwa ga mataki na gaba wajen samar da sashen kula da harkokin diflomasiyyar ƙungiyar ta EU. Wannan sashen da Turai ke shirin kafawa domin kula da harkokin wajen ta, na da zimmar taimakawa ƙungiyar ta ɓullo da sahihiyar manufar kula da ƙetaren ta, wanda zai kawo ƙarshen saɓanin da ake samu a tsakanin wakilan ƙungiyar, lamarin da kuma ke raunana ƙarfin ƙungiyar wajen ɗaukar matsayi akan lamuran da suka shafi ƙasa da ƙasa. Tuni dai Catherin Ashton ta yi nasarar samun goyon bayan hukumar tarayyar Turai da kuma ƙasashe mambobin ƙungiyar. Ana dai sa ran yarjejeniyar za ta samu amincewar majalisar dokokin ƙungiyar a lokacin wata babbar zaman taron da za ta gudanar cikin watan gobe - idan Allah ya kaimu a birnin Strabourg.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu