1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sake farfado da ginar gargajiya a Nijar

Issoufou Mamane/GATAugust 10, 2016

A wani matakin fafado da gine-gine irin na gargajiya, a jihar Tahoua ta jamhuriyar Nijer, wani matashi ne ya maida hankali ga yin gini irin ta dutsi da ta yi fice tun a lokacin mulkin mallaka

https://p.dw.com/p/1JfPG
Palast des Emirs von Damagaram in Zinder, Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Alhaji Salifu Atamaka, wanda aka fi sani da sunan Salah magini, wani matashi ne dan kimanin shekaru 40 da haifuwa, wanda ya yi fice a nan jihar Tahoua gurin sarrafa dutsi a matsayin birgi ko kuma bulo da yake gini da shi, aikin da ya ce ya gaje shi ne daga mahaifinsa ya kuma dau matakin farfado da shi ne a dalilin kawata gari da ginin ke yi. Shi dai Salah magini, ya ce ginin na dutsi na tattare ne da dimbin tarihi, abunda ya kara bashi kwarin gwiwar farfado da shi.

Abakar Abdu, na daga cikin matasan da suka samu koyon wannan aikin ginin dutsi, ya kuma shaida irin tasirin da wannan gini take da a yanzu a idon al'unmma da kuma irin matakan da ginar take bukata wajen aiwatar da ita.

Mann auf einem Esel in Zinder, Niger
Hoto: DW/M. Kanta

To ganin irin dimbin tarihin dake tattare da makamantan wadannan gine-ginen ne jama'a ke matukar nuna shawarsu a kansu tare da neman komawa kan yayin mallakarsu a wannan zamani inji alhaji Abdullahi wani mazaunin birnin Tahoua da ke da irin wannan ginin.

Sai dai Salah maginin ginar ta dutsi ya ce babbar matsalar da yake fama da ita a halin yanzu ita ce ta rashin wadatattun kayan aiki da kuma musamman ta rashin wallafa aikin nasa daga gwamnati domin jama'a su san shi.