Sakatariyar harkokin wajen Amurka ta ja kunnen kasar Sudan | Labarai | DW | 27.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakatariyar harkokin wajen Amurka ta ja kunnen kasar Sudan

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice tayi kira da a gagguta tsagaita wuta a yankin darfur na Sudan ta kuma bukaci gwamnatin Sudan din da ba tare da bata lokaci ko gindaya wasu sharudda ba ta amince da aikewa da dakarun Majalisar Dinkin Duniya zuwa yankin na Darfur.

Tace gwamnatin Sudan tana da zabi tsakanin amincewarta ko kuma ta fuskanci arangama da kasa da kasa.

Condoleeza Rice ta gargadi Sudan game da abubuwa da zasu iya biyo baya da bata faiyace su ba,muddin dai Sudan din taki amincewa da dakarun na Majalisar Dinkin Duniya.

Rice tace shugaban Amurka G.Bush ya fadawa shugaban Sudan Omar al Bashir cewa Amurka a shirye take ta sake duba dangantaka tsakaninsu,haka kuma mahukuntan kasar Amurkan sun kusa cimma yarjejeniya kann lakabawa gwamnatin Sudan takunkumi.

Sakatariyar ta Amurka ta ce muddin dai Sudan taci gaba da yakar jamaarta,tare da kalubalanatar kungiyar AU da sauran kasashe to ta shafawa kanta ruwa.