Sakatariyar harkokin wajen Amurka ta isa Romania | Labarai | DW | 06.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakatariyar harkokin wajen Amurka ta isa Romania

A ci gaba da ziyarar da take a nahiyar turai, a yanzu haka sakatariyar harkokin wajen Amurka wato CR na kasar Romania.

Kafafen yada labaru na kasar sun rawaito Rice na yabawa kasar ta Romania bisa namijin kokarin da suka nuna na tabbatar da yanci ga Alummar kasar Iraqi da Afghanistan ta hanyar aikewa da dakarun sojin kiyaye zaman lafiya izuwa kasashen.

Kafin dai isar ta izuwa Romania, a yammacin yau Rice ta gana da Shugabar gwamnatin Jamus wato Angela Merkel, a inda shugabannin biyu suka cimma matakin aiki kafada da kafada don warware takaddamar data taso game da aiyukan hukumar CIA a nahiyar Turai.

Cimma wannan yarjejeniya tazo ne a yayin da gwamnatin ta Jamus ke bukatar cikakkikyar amsa daga mahukuntan na Amurka game da zargin da ake cewa hukumar leken asiri ta CIA na mallakar wasu gidajen azabtar da fursunoni a wasu kasashe a nahiyar ta turai.

Ba a dayan haka akwai kuma zargin da akeyiwa hukumar ta CIA cewa tana amfani da wasu filayen jiragen sama na Jamus wajen yin jigilar fursunonin izuwa asirtattun gidajen azabtarwar dake wasu kasashe a gabashin Turai.