1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakatariyar harkokin wajen Amurka ta isa Masar

March 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuP3

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice ta isa kasar Masar domin tattaunawa da shugabanin kasar da nufin farfado da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Palasdinawa da Israila.

Rice zata gana da shugabanin Jordan da na saudiya da Masar da kuma haddaiyar daukar larabawa a birnin Aswan na kasar ta Masar.

Wannan itace ziyarar Rice ta farko tun bayan kafa sabuwar gwamnatin hadin kann Palasdinwa,wadda ta hada da membobin kungiyar Hamas dana Fatah da ake ganin suke da matsakaicin raayi.

A halinda ake ciki kuma sakataren MDD Ban Ki Moon bayan gawanrsa da shugaban kasar Masar Hosni Mubarak ya roki sabuwar gwamnatin ta Palasdinawa da ta ba marada kunya ta bin bukatun kasashen duniya ta maince da kasancewar kasar Israila.