Sakatariyar harkokin wajen Amirka za ta kai ziyara a Gabas Ta Tsakiya a ran juma’a mai zuwa. | Labarai | DW | 19.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakatariyar harkokin wajen Amirka za ta kai ziyara a Gabas Ta Tsakiya a ran juma’a mai zuwa.

2. Sakatariyar harkokin wajen Amirka z ata kai ziyara a Gabas Ta Tsakiya a ran juma’a mai zuwa.

A yunƙurin da ake yi na kwantad da ƙurar rikici a yankin Gabas Ta Tsakiya, sakatariyar harkokin wajen Amirka, Condoleeza Rice, za ta fara kai ziyara a yankin tun daga ran juma’a mai zuwa. Rahotannin da ke iso mana daga birnin Washington sun ce, tsai da shawarar kai ziyarar ta Rice, ya biyo bayan tattaunawar da ta yi ne jiya da babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan a birnin New York.

A wata sabuwa kuma, Isra’ila ta ce za ta ci gaba da ɗaukinta a Lebanon har zuwa lokacin da ƙungiyar Hizbullahi ta sako sojojinta biyu da ta yi garkuwa da su kuma ta daina harba mata rokoki daga Lebanon ɗin. Firamiyan Isra’ilan Ehud Olmert ne yqa bayyana haka, yayin da yake ganawa da jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda ke ƙoƙarin shiga tsakani don sasanta rikicin. Wani binciken jin ra’ayin jama’a da aka gudanar na nuna cewa kusan kaqshi 86 cikin ɗari na ’yan Isra’ilan ne ke goyon bayan matakan da gwamnatinsu ke ɗauka kan Lebanon.