Sakatariyar harkokin wajen Amirka na ci-gaba da rangadin kasashen Asiya | Labarai | DW | 19.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakatariyar harkokin wajen Amirka na ci-gaba da rangadin kasashen Asiya

Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta isa babban birnin kasar KTK, Seoul a mataki na biyu na rangadin da take kaiwa kasashe 4 na nahiyar Asiya. Manufar ziyarar tat ta ita ce matsawa KTA lamba bayan gwajin makamin nukiliya da ta yi. Bayan tattaunawar da ta yi da ministan harkokin wajen Japan Taro Aso a Tokyo, Dr. Rice ta yi gargadi KTA da ka da ta kuskura ta sake yin wani gwajin makamin nukiliya. Tana wannan balaguro ne a Japan, KTK, Sin da Rasha da nufin shawo kan kasashen su aiwatar da takunkuman da MDD ta sanyawa gwamnatin Pyongyang. KTA ta bayyana takunkuman da cewa wani yaki ne aka kaddamar a kanta saboda haka zata mayar da martani akan kasashen da suka yi kokarin aiwatar da su.