Sakatariyar harkokin wajen Amirka Dr. Rice ta fara ziyara a kasar Rasha | Labarai | DW | 21.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakatariyar harkokin wajen Amirka Dr. Rice ta fara ziyara a kasar Rasha

Sakatariyar harkokin wajen Amirka C. Rice ta ki ta tabbatar da rahotannin da aka bayar cewa KTA ta ce ba zata sake yin gwajin makamin nukiliya ba. A lokacin da ta sauka a birnin Mosko Rice ta ce wakilin China na musamman Tang Jiaxuan ta tabo wannan magana ba a ganawar da suka yi. Da farko kamfanin dillancin labaraun KTK Yonhap ya rawaito cewar shugaban KTA Kim Jong Il ya fadawa wakilin na China cewar kasarsa ba zata sake yin gwajin makamin nukiliya ba. A ziyarar da ta fara kaiwa Mosko a yau, sakatariyar harkokin wajen ta Amirka zata gana da shugaban Rasha Vladimir Putin da ministan harkokin waje Sergei Lavrov da kuma ministan tsaro Sergei Ivanov kan yadda za´a tinkari KTA dangane da shirinta na nukiliya da ake takaddama a kai. Yanzu haka dai Amirka na kokarin ganin shawo kan kasashe su aiwatar da takunkuman da kwamitin sulhun MDD ya kakabawa KTA.