sakatarin harkoki wajen Amurka Condoleezza Rice ta amince da yarjejeniyar Beijing | Labarai | DW | 13.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

sakatarin harkoki wajen Amurka Condoleezza Rice ta amince da yarjejeniyar Beijing

Sakatarin harkokin waje na Amurka Condoleezza Rice ta yi na’am da yarjejeniya da aka cimma a Beijing,tsakainn kasashe 6 ,da aka fara tun ranar alhamis.

Pyongyong dai ta amince waje daukan matakin farko,wajen tsayar da shirin ta na makamashin nukiliya,domin ta sami mai da take matukar bukata,ko bunkasa tatalin arzikinta.

Rice ta ce wannan nasarar da aka cimma a bisa wannan yarjejeniya ya kasance ne kawai matakin farko domin ko a cewarta,akwai sauran rina a kaba.