Sakataren tsaron Amirka ya fara ziyara ta farko a kasashen Larabawa | Labarai | DW | 18.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakataren tsaron Amirka ya fara ziyara ta farko a kasashen Larabawa

Jim Mattis wanda tsohon sojan ruwan Amirka zai gana da shugabannin yankin ko da yake ba a bayyana irin batutuwan da za a mayar da hankali kai ba.

Brüssel NATO Treffen (Reuters/F. Lenoir)

Sabon sakataren tsaron Amirka Jim Mattis

Sakataren tsaron Amirka Jim Mattis ya isa Hadaddiyar Daular Larabawa a wannan Asabar, a wata ziyarsa ta farko yankin na Larabawa, wata guda da kama aikin.

An dai sa ran zai gana ne da Yerima Mohammad Bin Zayd Al Nahyan na yankin da kuma ministan tsaro Mohammad Al Bawardi.

Tsohon janar na sojan ruwan na Amirka wanda ya fafata yaki a kasashen Iraki da kuma Afghanistan, masanin yankin ne musamman lokacin da yake jagorantar wata runduna.

Ba a dai bayar da cikakkun bayanai kan batutuwan da zai tattauna kansu a ziyarar ba, wanda ke zuwa jim kadan bayan wadansu tarukan da ya halarta a Brussels na Belgium da kuma Munich na Jamus a wannan makon.

Hadaddiyar Daular ta Larabawa dai yanki ne mai muhimmanci a kokarin Amirka na yaki da kungiyar IS da ke kasashen Iraki da kuma Siriya.