Sakataren tsaron Amirka Donald Rumsfeld ya yi murabus. | Labarai | DW | 09.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakataren tsaron Amirka Donald Rumsfeld ya yi murabus.

2. Sakataren tsaron Amirka Donald Rumsfeld ya yi murabus.

Game da kayen da jam’iyyarsa ta Republicans ta sha a zaɓen majalisun Amirka da aka gudanara shekaranjiya, shugaba George W. Bush, ya fara ɗaukan matakan yi wa gwamnatinsa kwaskwarima, da sauke sakataren tsaron ƙasar Donald Rumsfeld daga muƙaminsa. Shugaban ya naɗa tsohon daraktan ƙungiyar leƙen asirin CIA, Robert Gates, don ya maye gurbin Rumsfeld. A lokacin yakin neman zaɓen dai ’yan jam’iyyar Democrats sun yi ta kakkausar suka ne ga yadda Rumsfeld ke tafiyad da yaƙin Iraqi da kuma manufofin gwamnatin shugaba Bush a wannan ƙasar. Hakan ne kuwa ya sa suka lashe zaɓen, abin da ya ba su damar samun rinjayi a majalisun ƙasar guda biyu, a karo na farko tun shekaru 12 da suka wuce. Da yake yi wa maneman labarai jawabi a fadar White House, shugaba Bush ya amince da cewar manufofinsa a Iraqi ba sa aiki kamar yadda ya tanadar.