Sakataren rundunar sojin Amirka Francis Harvey yayi murabus | Labarai | DW | 03.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakataren rundunar sojin Amirka Francis Harvey yayi murabus

Shugaban rundunar sojin Amirka mai kula da ayyukan farar hula Francis Harvey yayi murabus a dangane da wata takaddama da ta shafi rashin kulawa da sojojin kasar da suka jikata. Sakataren tsaron Amirka Robert gates ya ba da sanarwar murabus din na sakataren rundunar sojin Francis Harvey. Hakan dai ya zo kwana daya bayan an sallami shugaban cibiyar ba da magani ta rundunar sojin Amirka. A cikin makon jiya jaridar Washington Post ta bayyana halin da ake ciki a cibiyar ba da magani ta Walter Army Medical Center dake birnin Washington inda ake yiwa sojojin kasar da suka samu raunuka a Afghanistan da Iraqi, da cewa wasu dakuna dake cike da beraye da kyankyasai. Shugaba GWB ya yi alkawarin kafa wani kwamitin bincike mai zaman kanshi da zai bincike wannan lamari.