Sakataren MDD ya soki matakin Israila akan yankin Gaza | Labarai | DW | 30.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakataren MDD ya soki matakin Israila akan yankin Gaza

Sakataren Majalisar ɗinkin duniya Ban Ki-Moon ya soki Israila a game da rage samar da makamashin man Petur dana Gas a yankin zirin Gaza. A cikin wata sanarwa sakataren na Majalaisar ɗinkin duniya yace ɗaukar irin wannan mataki tamkar azabtar da ɗaukacin alúmar Falasɗinawa ne. Ita ma ƙungiyar tarayyar turai ta baiyana makamancin wannan damuwa. A ranar lahadin da ta wuce ne Israila ta fara aiwatar da matakin takunkumin akan yankin na Gaza, tana mai cewa ta ɗau matakan ne a matsayin martani ga harin rokoki da yan takifen Hamas ke kaiwa garuruwan Israilan. A waje guda kuma babban mai shariá na Israilan yace ko kaɗan gwamnatin bata da damar katse hasken wutar lantarki ga zirin Gaza ba tare da yin cikakken nazarin halin da zai jefa alúma mazauna yankin ba.