Sakataren MDD ya ja hankali ga tabarbarewar tsaro a Dafur | Labarai | DW | 22.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakataren MDD ya ja hankali ga tabarbarewar tsaro a Dafur

Sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan ya yi kashedi da tabarbarewar doka da oda a lardin Dafur na kasar Sudan. A saboda haka Kofi Annan ya yi kira ga gwamnatin da yan tawaye su yi kokarin cimma shawarwarin sulhu ya zuwa karshen wannan shekarar da muke ciki. A rahoton sa na wata wata da ya gabatarwa kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniyar, Kofi Annan yace an sami karuwar tarzoma da kashe kashen rayuka da kuma fyade a yankin na Dafur musamman a watanni biyu da suka gabata. Kofi Annan yace hanya daya ta sulhunta rikicin ita ce bangarorin su yi kokarin cimma yarjejeniya a shawarwarin sulhun da ake gudanarwa a Abuja karkashin inuwar kungiyar gamaiyar Afrika. A ranar Litinin mai zuwa ne dai zaá koma tattaunawar karo na bakwai a birnin Abujan Nigeria.