Sakataren MDD ya buƙaci Israila ta sake tunani | Labarai | DW | 20.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakataren MDD ya buƙaci Israila ta sake tunani

Sakataren Majalisar ɗinkin duniya Ban Ki-Moon ya yi kira ga Israila ta sauya shawara a game da sanarwar da ta bayar na baiyana zirin Gaza a matsyin ɗaya daga cikin yankunan yankin abokan gabar ta. Bugu da ƙari ya kuma yi kashedin cewa katse muhimman buƙatun rayuwa ga alúmar yankin ya sabawa dokokin ƙasa da ƙasa. Ministan harkokin wajen Israila Tzipi Livni ta ce Israila zata maida da martani ga dukkan wani hari da zaá kai ciki ƙasar ta daga Gaza. Tace to amma duk da haka Israila zata cigaba da samar da buƙarun da suka wajaba ga alúmar ta Gaza. Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas ya baiyana matsayin Israila da cewa mataki ne da zai azabtar da alumar Falasɗinawa baki ɗaya.