1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakataren Majalisar Dinkin duniya yayi gargadi game da barkewar rikici a Chadi

Gwamnatin kasar Chadi ta sassauto daga barazanar da tayi game da game da rikicin kasar,bayan yanke huldar diplomasiya da Sudan.

Shugaba Idris Deby

Shugaba Idris Deby

shugaba Idris Deby ya kara waadin katse dukkanin bututun mai da yace zai fara yau talata,zuwa karshen wannan wata,saboda sabani da babban bankin duniya game da kudaden fito na man fetur kasar har sai bankin ya saki kadarorin kasar da yake dakatar.

Chadin tace,jinkirta rufe bututun man,ya biyo bayan tayin da Amurka tayi ne na shiga tsakani cikin rikicin,wanda ya hada da wani kanfanin mai na Amurkan,wanda keda jarin dala biliyan 3.7 a kasar ta Chadi.

Shugaba Deby,wanda ke fuskantar juyin mulki daga yan tawayen da yace,Sudan na marawa baya,ya tabbatarwa da Majalisar Dinkin Duniya cewa,ba zai tilasatawa yan gudun hijira fiye da 200,000 da suke tsere daga tashe tashen hankula na Darfur komawa gida ba.

Komishinan kula da yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yace ya samu tabbaci daga shugaba Deby cewa ba zai kori yan gudun hijirar ba.

Wannan kuwa ya sassauta barazana da shugaban na Chadi yayi,bayan yanke huldar diplomasiya da Sudan ranar jumaa,ya kuma rufe bakin iyakarsu kwana daya bayan yan tawayen sun kai hari a babban birnin kasar N’Djamena,inda mutane da dama suka rasa rayukansu wasu kuma suka jikkata.

Shugaba Deby dai yana kokarin kare bore na soji tare da yunkurin kawo karshen mulkinsa na shekaru 16,kafin zaben shugaban kasa na ranar 3 ga watan mayu mai zuwa,inda zai sake tsayawa takara karo na uku.

Kasar Sudan dai ta karyata zargin goyon bayan yan tawayen,amma rikicin dai ya kawo zaman dar dar a yankin,wanda tuni yake cikin tashe tashen hankula na kan iyaka da kuma kwararowar yan gudun hijira daga Darfur.

A halin yanzu dai,sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan,ya nuna damuwarsa game da rikici tsakanin Chadi da Sudan,saboda haka ya bukaci Kungiyar Taraiyar Afrika da sauran kasashen yankin da suyi anfani da dama da suke da ita,domin kare babban rikici a yankin,wanda yace zai shafi sauran kasashe.

Tashe tashen hankulan da kuma barazanar katse mai da korar yan gudun hijira da Deby yayi,ya sanya tilas Majalisar Dinkin Duniya ta nemi kawo karshen rikicin shekaru 3 na yammacin Sudan,wanda yayi sanadiyar mutuwar dubban jamaa miliyoyi kuma suka tagaiyara.

 • Kwanan wata 18.04.2006
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu0Z
 • Kwanan wata 18.04.2006
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu0Z