1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakar gidan Gizo-gizo

Abba BashirMarch 19, 2007

Yadda Gizo-gizo yake saka gidan yanarsa

https://p.dw.com/p/BvUu
Gidan Yanar Gizo-gizo
Gidan Yanar Gizo-gizoHoto: AP

Gizo-gizo! Wata halitta ce daga nau’ukan kwari da Allah madaukakin Sarki ya halitta bisa hikima da ikonsa. Shi ‘Al-Khaliku’ ya fi kowa sanin dalilinsa na tsara dabi’un gizo-gizo a yadda suke, to amma ba shakka akwai ayoyi da hikimomi masu yawa tattare da irin tsari na musamman da wasu mu’ujizoji da Allah ya kebanci gizo-gizo da su, wanda dole hankali ya yarda cewa Allah ya yi su ne don su zamo ayoyi, kuma abin lura da tunani ga mutane.

Gizo-gizo mai suna Dinopis, yakware wajen iya farauta. Kuma Ba wai kawai yana sakar gidansa dan jiran fadowar abincinsa ba, sai dai yana saka wata karamar igiya da yake jefawa akan abincinsa yayin da yake son kamawa. Idan abincin nasa ya fado akan yanar-gidan, wato kamar kuda da dai sauransu, nan da nan sai wannan igiya ta nannade shi da sakar. Kwaron da wannan igiya ta kama , ba zai iya kubucewa ba, saboda Sakar, tayi sakuwar da idan kwaron yana kara dauruwa ita kuma tana kara shiryuwa. Kuma a lokacin da gizo-gizo yake kokarin killace abincinsa, sai ya daure kwaron da ya kama a matsayin abincinsa da wasu igiyoyin, kamar dai Matafiyi mai daure kaya, idan zai tafiya.

To abune mawuyaci ace gizo-gizo ya samu irin wannan fasaha kwatsam kamar yadda masana ilimin juyin halitta da’awa. Babban abin al’ajabin anan shine, gizo-gizo bashi da kwakwalwa balle ya koyi wannan aiki, ya kuma haddace, kuma ya rika yi yau da kullum.Babu wata makaranta ta firamare ko sakandare ko Jami’a da za’a ce anan ne gizo-gizo ya koyi fasahar saka gidansa,kuma wani abin mamaki shine, da gizo-gizon dake Jamus da na Amurka DA na Najeriya dama na ko’ina a cikin Duniya,sakar tasu iri daya ce, wajen kama da cika da kamala. Babu shakka wannan fasaha ta GIZO; halitacciya ce daga madaukakin Sarki Allah, mabuwayi a cikin ikonsa.

Babu shakka akwai muhimman Muhimman mu’jizozi a boye, tattare da sakar gizo-gizo. Zaren da Gizo,yake samarwa daga jikinsa, wanda yake da tsananin siranta,yafi wayar kafe kwari har sau biyar, wadda take da siranta dai dai da shi . Wata sifa da wannan zare yake dauke da ita, ita ce , duk jikinsa hasken fitila ne. Kuma masana ilimin kimiyya sun tabbatar da cewa, idan da za’a samu zare mai irin tsawon zaren da gizo-gizo yake sakawa,to ya isa ya iya zagaye duniya, kuma nauyin zaren ba zai wuce giram 320 ba. Anan ne masana ilimi suka yi nazarin gidan gizo-gizo,suka kuma kwaikwayi fasahar gizo, suka samar da hanyar sadarwar da a yau Duniya take takama da ita wajen cigaban kimiyya, wato hanyar sadarwa ta yanar-gizo wadda aka fi sani da Internet. Wanda sakamakon haka yasa Duniya yanzu ta zama kamar wani dan-karamin kauye, inda duk abinda ya faru ake iya sani cikin dan-kankanen lokaci.

Wata fasahar kuma itace, karfe, wanda ake samara dashi don aiki a masana’antu, daya ne daga cikin abubuwan da dan Adam yakera. Haka kuma, gizo-gizo daga jikinsa, yana iya samar da zaren da yafi karfe karfi. Matukar dai karfen yayi daidai da kaurin zaren na gizo.Sannan kuma ,Yayin da mutum yake samara da karfe, yana amfani dashi ne ta tsohon ilmi da fasahar Mutanen da; to wane ilmi da fasaha gizo-gizo yake dashi yayin da yake samara da nasa zaren?

To darasin da dan-adam zai iya dauka daga fasaha da hikimar da Allah ya baiwa gizo shine cewar,Dan adam ya yarda da cewa,Dukkan abinda Allah ya halitta, to bai halicce shi a banza ba, akwai wani dalili da Allah yasa ya yi wannan halitta.Domin duk da cewa, a Duniya ana ganin mafi raunin gida,shine gidan gizo-gizo, to amma Allah cikin hikimarsa, sai ya tsara cewar, da wannan hikima ta gizo ce, Dan-adam yau yake takama a Duniya.Kuma hakan yana nuna kenan, duk fasaha da dabarun da mutum yake da su, tuni gizo-gizo ya barshi a baya.