Sakamakon ziyarar Gambari a Myanmar | Labarai | DW | 04.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon ziyarar Gambari a Myanmar

Sakataren Majalisar ɗinkin duniya Ban ki-Moon yace jakadan sa na musamman Alhaji Ibrahim Gambari ya isar da sako mai karfi ga shugabanin mulkin sojin ƙasar Myanmar a dangane da dirar mikiyar da suka yiwa masu fafutukar cigaban dimokraɗiya. Sai dai kuma yace ba zai iya baiyana cewa ziyarar ta yi cimma biyan buƙata ba. Ban ki-Moon yace a ranar jumaá zai gana da kwamitin sulhun Majalisar ɗinkin duniyar domin shawarta matakin da zasu ɗauka a game da take haƙƙin bil Adama a Myanmar, yana mai cewa halin da ake ciki a ƙasar babban abin damuwa ne ga ɗaukacin ƙasashen duniya. A yau ne Ibrahim zai gabatarwa da sakataren Majalisar ɗinkin duniyar cikakken rahoton sakamakon ziyarar da ya kai zuwa Myanmar.