1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon Ziyarar Fischer A Sudan

July 13, 2004

Ko da yake ba a cimma tudun dafawa a shawarwarin da ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer ya gudanar da jami'an gwamnatin Sudan ba, amma ana fatan ci gaba da matsin kaimi akan fadar mulki ta Khartoum har sai ta dauki nagartattun matakai na shawo kan rikicin Darfur

https://p.dw.com/p/BviC

A hakika dai kasar Sudan bata cikin rukunin kasashen dake mahrabin lale da ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer. Tun kafin Fischer ya fara gudanar da shawarwarinsa a hukumance, wata jaridar kasar Sudan mai suna "Sudan Vision" dake fita da harshen Turanci ta fara kalubalantarsa da cewar wai "Mu a nan Sudan ba ma fuskantar ta’asar kisan kare dangi" kuma "wai shin Fischer me kake nema ne a nan kasar?" Bayan haka jaridar ta ci gaba da zargin cewar wai, Jamus, "babbar daular nahiyar Turai" tana ba da taimakon kudi ga ‚yan tawayen dake yakar gwamnati a lardin Darfur. Kafofin farfaganda na kasar ta Sudan sun yi bakin kokarinsu wajen ganin kowane dan-jaridar Jamus dake wa ministan harkokin wajen rakiya ya samu kofin wannan jarida dake musu barka da isowa. Dangane da Fischer kuwa wani dan jaridar kasar Sudan ne ya nace akan fuskantarsa da tambayar wai shin me ya sa Jamus ke rufa wa ‚yan tawayen Sudan baya. Duk wanda ya lura da fuskar Fischer zai gane cewar ta kunshi batutuwa iri dabam-dabam lokacin da yake fatali da wannan harin da aka kai masa. Ta la’akari da wannan mummunan yanayin da aka shiga sai aka ajiye maganar diplomasiyya gefe guda. Fischer ya ce duniya ta gaji da gafara sa ba ta ganin ko kafo. Abu mafi alheri shi ne gwamnatin Sudan ta tashi tsaye wajen magance rikice-rikicenta a maimakon alkawururruka na fatar baki. Tilas ne a shawo kan mawuyacin halin da ake ciki a Darfur. A nasu bangaren wakilan gwamnatin Sudan sun mayar da martani da cewar gwamnati na bakin kokarinta, kuma tilas ne a samu hakuri. Dadin dadawa kuma gwamnatin Sudan ba ta so a rika yi mata shisshigi a al’amuranta na cikin gida. An ci gaba da fama da wannan sabani hatta a shawarwari na bayan fage da aka gudanar tsakanin Fischer da jami’an gwamnatin Sudan. A sakamakon haka ministan harkokin wajen na Jamus yake ganin cewar a yanzu ba abin da ya rage illa a kakaba wa Sudan matakan takunkumi kuma Jamus zata ba wa wannan manufa goyan baya a kwamitin sulhu na MDD. Wadannan matakai zasu iya hadawa da takunkumin karya tattalin arzikin kasa da haramta sayarwa da gwamnatin Sudan makamai. Za a saurara wa fadar mulki ta Khartoum a ga irin yunkurin da zata yi wajen warware matsalar nan da wasu ‚yan makonni kadan masu zuwa. Kuma ko da yake kwalliya ba ta mayar da kudin sabulu a game da ziyarar ta Fischer ba, amma akalla ziyarar ta bayyanar a fili cewar kasashen Turai sun sa ido wajen ganin yadda makomar mazauna yankin Darfur zata kasance. Za a ci gaba da yi wa gwamnatin Sudan matsin lamba har sai an ga abin da ya ture wa buzu nadi. Abin takaici guda daya shi ne kasancewar wannan matsin lamba ta zo a makare saboda a yanzu haka ana sauraron saukar damina, wacce zata kara tsawwala mawuyacin halin da ake ciki a lardin na Darfur.