1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakamakon Ziyarar Bush A Brussels

Tare da nanata kiran hadin kai tsakanin Amurka da kawayenta na nahiyar Turai shugaban Amurka G.W. Bush ya kammala ziyararsa a birnin Brussels

Shugaba Bush a taron kolin kungiyar tsaro ta NATO

Shugaba Bush a taron kolin kungiyar tsaro ta NATO

Ana iya cewar kwalliya ta mayar da kudin sabulu a game da ziyarar shugaban Amurkan George W. Bush ga nahiyar Turai, idan har da gaske yake a game da neman sararawar al’amura a dangantakar Amurka da kawayenta na Turawa. Ba tare da yarfe gumi ba, shugaba Bush ya shawo kan shuagabannin kasashen Turai domin goya masa baya, abin kuwa da ya hada har da wadanda a zamanin baya suke sukan lamirin manufofinsa. Mai yiwuwa sun farga ne cewar ba su da zabi, saboda tilas ne a ci gaba da damawa da kasar Amurka a siyasar duniya inda zaki ko da tsami, kamar yadda aka lura a shekaru hudun da suka wuce. Akalla dai shugaba Bush sosa wa Turawa kawayen Amurkan daidai inda ke musu kaikai, inda yake bayyana musu cewar kasar tana bukatar hadin kansu akan manufa. Amma fa wajibi ne su yi taka tsantsan, su yi sara tare da duban bakin gatarinsu. Domin kuwa abin lura shi ne shugaba Bush yayi wa kasashen Turai tayin shiga a dama da su a matakan tabbatar da walwala da zaman lafiya, wadanda suka fara daga Afghanistan ya zuwa kasar Iraki, wadanda kuma ba wanda ya san lokacin da zasu kawo karshensu. Amma a daya bangaren shugaba Bush bai fito fili yayi bayani a game da ainifin wanda zai ja akalar wadannan matakai ko yayi tasiri akansu ba. Duk wanda yayi bitar jawabin da shugaba Bush ya gabatar a birnin Brussels a game da manufofin na Amurka zai iya tantance cewar manufarsa dai shi ne, duk wanda ya ki ba wa Amurka goyan baya ya zama abokin adawarta. Ana iya fahimtar ainifin alkiblar da shugaban ya fuskanta idan aka saurari bayanan da ya rika yi wa manema labarai, inda yake amsa tambayoyinsu kai tsaye ba tare da wani rubutaccen jawabi da aka shirya tun farko ba. Kamar dai takunkumin haramcin sayarwa da China makamai da yarjejeniyar Kyoto da kotun kasa da kasa, dukkan wadannan muhimman batutuwa ne da shugaban bai tabo su a cikin jawabinsa ba. Ko shakka babu a game da cewar kungiyar kawancen tsaro ta NATO tana bukatar nagartattun matakai domin tinkarar matsalolin da suka hada da na yankin gabas ta tsakiya, amma fa har yau akwai sabani tsakanin Amurka da kawayenta na nahiyar Turai, a game da wadannan matakai. Shi dai shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder bai yi wata rufa-rufa ba yana mai bayyanarwa a fili cewar wajibi ne a ba wa kasashen Turai karin fada a ji a manufofin kungiyar ta NATO. Kuma ko da yake shugaba Bush ya hakikance da haka, amma kamar yadda muka yi bayani tun farko a tarukan da ya gudanar da manema labarai, shugaban na Amurka, daidai da sakatariyarsa ta harkokin waje Condoleeza Rice, wacce ta kawo ziyarar share fage, sai da ya rika batu a game da kakkarfan matsayi da Amurka ke da shi a matsayinta na babbar daular duniya, amma tana bukatar goyan bayan kasashen Turai ne kawai domin cimma burinta. Ta la’akari da haka ya zama wajibi kasashen na Turai su yi taka tsantsan saboda ita Amurka manufarta a game da wannan kawance shi ne ta cimma biyan bukatunta.