Sakamakon ziyara tawagar dattawan ƙasa da ƙasa a Darfur | Labarai | DW | 04.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon ziyara tawagar dattawan ƙasa da ƙasa a Darfur

Tawagar nan ta dattawan ƙasa da ƙasa, ta kammala rangadin da ta yi a yankin Darfur na ƙasar Sudan, da zumar shiga tsakani a rikicin da ke wakana a wannan yanki.

Tawagar da Desmond Tutu ɗan ƙasar Afrika ta kudu ya jagoranta, ta ƙunshi manyan mutane 4, masu ƙima a idon dunia, wanda kuma su ka taka rawar gani, ta fannin samar da masalaha, a rigingimu daban-daban da su ka ɓarke a cikin wannan dunia.

A sakamakon wannan rangadi, dattawan,sun bayyana mahimanci anfani da yarjejeniyar sulhun da ɓangarori daban-daban masu gaba da juna a Darfur su ka cimma, a shekara ta 2005, a birnin Abuja na Tarayya Nigeria.

A ɗaya wajen su bukaci a gaggauta tura rundunar kwantar da tarzoma ta haɗin gwiwa, tsakanin Majalisar Ɗinkin Dunia da ƙungiyar Tarayya Afrika a yankin na Darfur.

Sannan wannan tawaga, ta yi kira ga ɓangarorin da ke da hannu a cikin wannan rikici, su bada damar shirya zaɓen yan malajisun dokoki a yankin, a shekara ta 2009, kamar yadda yarjejeniyar da aka cimma ta tanada.