sakamakon zaben yan majalisun dokoki a kasar Labanon | Siyasa | DW | 30.05.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

sakamakon zaben yan majalisun dokoki a kasar Labanon

sabon jini ya shigo fagen siyasar kasar Labanon,wanda a yanzu haka ake kallon sa a matsayin wanda zai kawo juyin juya hali a fagen siyasar kasar

default

Ya zuwa yanzu dai wannan zabe ya bawa dan tsohon faraministan kasar wato Rafik Hariri gagarumar nasara.

Rahotanni dai a yanzu haka na nuni da cewa kusan dukkannin kujerun yan majalisar dokokin birnin Beirut goma sha tara jamiyyar Saad Hariri ce ta lashe su da gagarumin rinjaye.

Zaben wanda ya zuwa yanzu bayanai suka shaidar da cewa shine irin sa na farko da aka taba gudanarwa a kasar ba tare da dakarun sojin kasar Syria a cikin kasar ta Labanon ba.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa zaben na birnin Beirut ya kasance na farko daga cikin zabubbuka da aka shirya gudanarwa daga zango izuwa zango.

Duk da cewa rahotanni sun shaidar da cewa ba a fito yadda yakamata ba a lokacin wannan zabe na jiya lahadin,Saaad Hariri na ganin cewa akwai alamun samun nasara daga bangaren jamiyyar tasu.

Bisa kuwa wannan nasara da jamiyyar ta Saaad Haririn ta samu dan na tsohon faraministan kasar ya bayyana cewa wannan nasara bata wani bace illa ta marigayi Rafik Hariri da kuma iyalan sa.

Saad Hariri mamshakin dan kasuwa mai shekaru 35,a yanzu haka ya kasance sabon jini ga harkokin siyasar kasar ta Labanon,wanda a yanzu zabi ya rage gareshi ko dai ya tsaya takarar neman faraministan kasar ko kuma akasin hakan.

Kafafen yada labaru na kasar sun rawaito mutanen birnin na gudanar da bukukuwan murna iri daban daban sakamakon wannan nasara da jamiyyar dan tsohon faraministan ta samu.

Game da sakamakon zaben sakataren mdd Kofi Anan ya bayyana fatan sa da cewa Allah yasa sakamakon zaben ya zama shine danba na dasa ayar ci gaban tafarkin dimokradiyya a fadin kasar ta Labanon baki daya.

Kofi Anan yaci gaba da cewa babu koja wan nan zabe na jiya lahadi zai taimakawa yan kasar ta Labanon kara fuskantar mulkin na dimokradiyya na yadda zasu dauki matakin bunkasa ta a fadin kasar baki daya.

Bugu da kari sakataren na mdd ya kuma jinjinawa mahukuntan na labanon bisa irin na namijin kokarin da suka nuna na tsara wannan zane da kuma gudanar dashi yadda aka tsara shi ba tare da bata wani lokaci ba.

A karshe Kofi Anan yayi fatan ragowar zabubbukan za a gudanar dasu bisa gaskiya da kuma adalci kamar yadda aka tsara su.

A waje daya itama kungiyyar tarayyar Turai wato Eu ta yaba ne game da yadda wan nan zabe na birnin na Beirut ya gudana ne da cewa abun sai dai Allah son barka.

A cewar shugaban tawagar ta Eu da suka sa ido game da yadda wannan zabe ya gudana,wato Jose Ignacio cewa yayi bisa dukkannin alamu akwai adalci da gaskiya game da yadda aka gudanar da zaben da kuma kidayar kuriun.

Ya zuwa yanzu dai rahotanni sun shaidar da cewa cikakken zaben yan majalisun dokokin kasar zai fita ne a ranar goma sha tara ga watan yuni na wannan shekara da muke ciki bayan an kammala dukkannin zabubbukan na zango izuwa zango kamar yadda aka shirya su.

 • Kwanan wata 30.05.2005
 • Mawallafi ibrahim sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvbe
 • Kwanan wata 30.05.2005
 • Mawallafi ibrahim sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvbe