1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaben shugaban kasar Polland zagaye na biyu

October 24, 2005
https://p.dw.com/p/BvO9

A daren jiya ne a kasar Polland a ka bayana sakamakon zaben shugaban kasa zagaye na 2, da a ka gudanar jiya lahadi, a fadin kasar baki daya.

A sakamakon wannan zabe Lech Kazynski, mai ra´ayin mazan jiya, ya zama saban shugaban kasar Polland ,bayan ya lashe zaben da kashi 55 dadugu 44 bisa dari.

Hukumar zaben kasar ,ta bayyana cewa kashi fiye da 50 bisa 100,na al´ummar da ya cencenta ta kada kuri´a, ta gudanar da zaben.

Saidai, a wani mataki na ba zata, dan takara da ya fi samun yawan kuri´u a zagaye na farko, wato Donald Tusk, ya ga samu ya ga rashi,a yayin da ya tashi da kashi 44 bisa 100, na jimmilar kuri´un da aka kada a zaben na jiya.

Jam´iyun 2 da su ka shiga zagaye na 2 a zaben shugaban kasar Poland na da alkibla daya, a na sa ran kuma za su gama karfi, domin gudanar da aikin tada komadar tattalin arzikin kasar Polland.

Saban shugaban kasar zai cenji Alexander Kwasniewski, da ya jagoranci kasar Polland a tsawon shekaru 10.