1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zaben shugaban kasar Belarus

Belarus

Shugaba Alexander Lukashenko na Belarus ,ya lashe zaben daya gudana ranar lahadin daya gabata da samun kashi 83 daga cikin 100 na yawan kuriu da aka kada.Hukumar zaben kasar ta sanar da hakan yau bayan kammala kidayan dukkan kuriu da aka kada ayayin zaben na Lahadi.Shugaba Lukashenko ,wanda ya samun nasarar zarcewa a wannan kujera tasa a karo na uku,ya doke sauran abokan takaran nasa wadanda suka samu sauran kuriun.Adangane da hakane sakataren hukumar zaben kasar Nikolai Lozovik yace zaa rantsar da shugaba Alexander Lukashenko ranar 31 ga wannan wata,inda ya kara dacewa kashi 92.9,na wadanda suka cancanci zabe a Belarus din ne suka kada kuriunsu.

Amurka da kungiyar gamayyar turai dai sunyi Allah wadan zaben,ayayinda daruruwan masu adawa da Shugaba Lukashenko ,ke zanga zanga tun daga ranar litinin.Yadai jagoranci wannan kasa dake gabashin turai ,tsakanin Rasha da Eu ,da karfin gaske na tsawon shekaru 12 da suka gabata.

 • Kwanan wata 23.03.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu7L
 • Kwanan wata 23.03.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu7L