Sakamakon zaben Maroko | Labarai | DW | 08.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zaben Maroko

Sakamakon zabe daga kuriu da aka kada a zaben yan majalisar dokoki a moroko jiya na nuni dacewa,jammiiyyar masu tsattsauran raayi ta Istiqlal ce ke jagoranci ,bayan kidaya sama da rabin kuriun da aka kada awannan masarautar.Jammiiyyar ta Istiqlal a yanzu nada rinjaye da kujeru 22,sai kuma jamiiyyar akidar musulunci ta JPD dake da 19,sai Rally of independents dake biye da kujeru 18.

Ayayinda sauran kujerun suka rarrabu tsakanin kananan jammiiyyu na marokon.A gobe da maraice ne ake saran cewa maaikatar harkokin cikin gida na kasar ta Maroko,zata gabatar da sakamako na karshen zaben na yan majalisa.