Sakamakon zaben majalisa a Bahrain | Labarai | DW | 26.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zaben majalisa a Bahrain

Yan adawa na darikar shia na kasar Bahrain,sun sanar da samun nasaran lashe kujeru 16 daga cikin 40,a zaben yan majalisar dokoki da akesaran sanar da sakamakonsa a ayau.Idan har sakamakon ya tabbatta,yan darikar shian zasu samu dama taka rawa a harkokin siyasar wannan kasa dake karkashin,masarautar yan Sunni,koda yake shugaban kungiyar musulmin kasar ta Al-Wefaq Fahim Abdullah,ya bayya shakku dangane da wani tasiri da sakamakon zaben zaiyi a harkokin siyasar kasar. Sai dai yayi gargadin cewa babu zasu amince dayin magudi adangane da sakamakon zaben majalisar dokokin da aka gudanar jiya ba.