Sakamakon Zaben Jihohin Brandenburg Da Sachsen A Nan Jamus | Siyasa | DW | 20.09.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakamakon Zaben Jihohin Brandenburg Da Sachsen A Nan Jamus

A karo na farko bayan watanni da dama da suka wuce jam'iyyar SPD ba ta fuskanci koma baya a zabubbukan da aka gudanar a jihohin gabacin Jamus guda biyu a jiya lahadi ba, a yayinda a daya bangaren murnar CDU ta fara komawa ciki kamar yadda sakamakon zabubbukan ya nunar

Ta dai faru ta kare. Domin kuwa a jiya lahadi an gudanar da zabe a jihohin Sachsen da Brtandenburg dake gabacin Jamus, inda a karo na farko jam’iyyar SPD da ta sha fama da koma baya a sauran zabubbukan da aka gudanar, ba ta yi wata asarar kuri’u ta a zo a gani ba, lamarin da ya sanya jami’anta suka fara cika baki a game da cewar sannu a hankali jam’iyyar ta fara farfadowa akan manufa. Ko shakka babu kuwa game da cewar farin jini da gwamnan jihar Brandenburg ke da shi ya taka muhimmiyar rawa a game da wannan ci gaba. Dangane da CDU kuwa, wacce ta samu koma baya na kashi 6%, bisa ga dukkan alamu masu jefa kuri’ar sun ankara ne da cewar ita ma fa tana da rabonta na alhakin matakan garambawul da ake wa gwamnati tofin Allah tsine akansa.Domin kuwa maganar ta garambawul ta taka muhimmiyar rawa a yakin neman zaben jihohin guda biyu. Wannan ma shi ne ainifin abin da ya taimaka jam’iyyar PDS ta samu ci gaba. Jam’iyyar ka iya shiga hadin guiwa da SPD, amma bisa ga dukkan alamu hadin guiwar zata wanzu ne tsakanin SPD da CDU. A can jihar Sachsen dai CDU tayi asarar gagarumin rinjayen da take tinkafo da shi, inda ta samu koma bayan kashi 15% idan aka kwatanta da zamanin baya. Ba shakka akwai wadanda zasu nemi dora wa gwamnan jihar Georg Milbradt laifin wannan koma baya. Domin kuwa baya da farin jini irin shigen magabacinsa Kurt Biedenkopf. Kuma ko da yake jam’iyyar FDP tayi ba zata wajen samun kafar shiga majalisar jihar ta Sachsen, amma duk da haka wannan ci gaba ba zai wadatar domin kafa mulkin hadin guiwa tsakaninta da CDU a wannan jiha ba. A yanzu dai an dokata a ga yadda zata kaya a wannan jiha, inda a zamanin baya CDU ke da kakkarfan angizo. Akwai yiwuwar kafa mulkin hadin guiwa tsakaninta da SPD. A takaice, jam’iyyun dake madalla da sakamakon zaben, wadanda za a iya cewa matakan garambawul na gwamnati sun zama tamkar gobarar titi a garesu su ne jam’iyyun dake da zazzafan ra’ayin kyamar baki, inda a jihar Brandenburg jam’iyyar DVU ta samu shiga majalisa, sannan a can Sachsen kuma jam’iyyar NPD ta cimma kashi tara cikin dari na jumullar kuri’un da aka kada. Wadannan jam’iyyun dake da zazzafan ra’ayin kyamar baki da adawa da safin tsarin mulkin demokradiyya sun samu ci gaba ne sakamakon tofin Allah tsine da suke wa matakan na garambawul, lamarin da ya ba su farin jini tsakanin jama’a. Kuma ko da yake dukkan jam’iyyun guda biyu ba su da wasu tsayayyun tsare-tsare na siyasa da suka sa gaba, amma wannan nasarar tasu, abu ne da ba makawa a damu da shi. Domin kuwa wannan abu ne dake yin nuni da yadda mutane suka fara tsarguwa da safifin tsarin mulkin demokradiyya a nan kasar sakamakon gazawar da ‚yan siyasarta suka yi wajen shawo kan matsalolin dake addabar jama’a a harkokin rayuwa ta yau da kullum. Amma fa yayata akidar kyamar baki ba zai tsinana kome wajen magance wadannan matsaloli ba, wannan shi ne abun da ya kamata a wayar da jama’a game da shi.