SAKAMAKON ZABEN JIHOHI A FARANSA YA SANYA GWAMNATIN SHUGABA CHIRAC CIKIN WANI MAWUYACIN HALI | Siyasa | DW | 30.03.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

SAKAMAKON ZABEN JIHOHI A FARANSA YA SANYA GWAMNATIN SHUGABA CHIRAC CIKIN WANI MAWUYACIN HALI

A zaben jihohin da aka yi a Faransa, jam'iyyun `yan mazan jiya na shugaba Jacques Chirac, sun sha gagarumin kaye. A cikin jihohi 22 da aka yi zaben, jiha daya tak ce kawai jam'iyyun suka sami rinjayi. A sauran jihoh 21, jam'iyyun gurguzu, da na kwaminis da na masu fafutukar kare muhalli ne suka ci nasara.

Shugaba Jacques Chirac na Faransa, a yakin neman zabe.

Shugaba Jacques Chirac na Faransa, a yakin neman zabe.

A kasar Faransa, wanda ya ci zabe a karo na farko, babu shakka shi zai sha kaye a wani zagayen kuma. Duk da cewa, wannan furucin ba rubutacciyar doka ba ce, amma haka lamarin yake a kasar. A lokacin da jam’iyyar gurguzu ke mulki a Faransan, ita ta ke shan kaye a zabuka daban-daban. Ta hakan ne kuwa a cikin shekara ta 2002, shugaba Jacques Chirac, ya sami gagarumin rinjayi a zagaye na biyu na zaben shugaba kasar da aka yi, inda ya tsaya takara da mai tsatsaurar ra’ayin nan Jean-Marie Le pen. Kazalika kuma, jam’iyyar shugaban ce ta lashe zaben majalisar dokokin kasar, da rinjayin kashi biyu bisa uku na kujerun majalisar.

Amma sai ga shi a zaben jihohi da aka yi a karshen mako, jam’iyyun gurguzu da makamancinsu ne suka ci nasara. Masharhanta dai na ganin cewa, sakamamkon zaben na nuna rashin amincewar jama’a ne da manufofin da gwamnatin shugaba Chirac ta sanya a gaba. A yunkunrin da Firamiya Jean-Pierre Raffarin ke yi na yi wa tsarin tattalin arzikin kasar garambawul dai, ya tabo bangarori daban-daban, wadanda kuma a halin yanzu ke nuna bacin ransu ga matakan da yake dauka. Masu bincike da masana kimiyya da dama sun yi murabus daga mukamansu saboda a nasu ganin, ba sa samun tallafin gwamnatin kuma. Ma‘aikatan kafofin al’adu na kasar kuma na ta yajin aiki. Kai har `yan sanda, da ma’aikatan kafofin kiwon lafiya, da malaman makaranta da `yan kwana-kwana, duk sun yi zanga-zanagar nuna bacin ransu ga matakan tsimin gwamnatin a kan titunan manyan biranen kasar. Bugu da kari kuma, marasa aikin yi na cikin wani hali ne na takaici, inda ba su da wata fatar samun aiki kuma a kasuwar kwadago. A takaice dai, za a iya cewa, garambawul din da gwamnatin Faransan ke yi, bai sami karbuwa a bainar jama’ar kasar ba.

A halin yanzu dai, jira ake yi a ga matakan da shugaba Chirac zai dauka bayan zaben. Har ila yau dai, jam’iyyarsa ce ke da rinjayi a majalisar dokokin kasar. Ba za a sake wani zaben `yan majalisar ba, sai a cikin shekara ta 2007. A cikin wadannan shekaru 3 dai, shugaba Chirac na da lokacin yi wa manufofinsa gyara don su sami amincewar al’umman kasar. Amma wasu masharhanta kuma na ganin cewa, sakamakon zaben ya raunana matsayin Jacques Chirac tamkar shugaban kasa. An ma fara yada rade-radi, kan wanda zai gaje shi a fadar Elysée. A cikin wadanda ake ganin za su nuna sha’awar gadan shugaban kuwa, har da Nicolas Sarkozy, ministan harkokin cikin gidan kasar na yanzu.

Amma babu wanda kafofin sadaswa suka fi mai da hankali a kansa yanzu, kamar Firamiya Jean-Pierre Raffarin. Saboda bisa dukkan alamu, bayan wannan kayen da jam’iyyun gwamnatin suka sha, yana cikin wadanda za su rasa mukamansu, idan shugaba Chirac ya tsai da shawarar yi wa gwamnatinsa garambawul. Abin da Faransawa ke neman sani yanzu shi ne, wai shin gwamnatin za ta ci gaba da aiwatad da manufofin yi wa tsarin tattalin arzikin kasar garambawul ne kuwa, bayan sakamakon da aka samu a wannan zaben ?

Firamiya Raffarin dai, a farkon jawabin da ya yi bayan an gabatad da sakamakon zaben, ya bayyana cewa ya ji sakon da jama’ar kasar ke niyyar ba shi, ta yadda suka ka da kuri’unsu. Amma masana harsuna da kuma masu sukar lamiri, sun nuna bambancin da akwai tsakanin kalmomin "entendre" (wato ji ) da kuma "écouter"(wato saurara) a faransance. A nasu ganin dai, ba écouter firamiyan ke nufi ba a cikin jawabin da ya yi. Amma ba da fiffiko ga sauraren ra’yin jama’a, maimakon ji kawai, shi ne zai fi zamewa wani abin fa’ida ga Firamiyan da kuma sauran mahukuntan birnin Paris.

 • Kwanan wata 30.03.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvky
 • Kwanan wata 30.03.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvky