1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon Zaben Jihar Saarland

September 6, 2004

Jam'iyyar CDU ta samu gagarumin rinjaye a zaben da aka gudanar a jihar Saarland a jiya lahadi.

https://p.dw.com/p/Bvgl
Gwamnan jihar Saarland Peter Müller dan jam'iyyar CDU
Gwamnan jihar Saarland Peter Müller dan jam'iyyar CDUHoto: AP

Wani abin lura dai a game da sakamakon zaben na Saarland shi ne kasancewar ko da yake yawan masu ikon kada kuri’a a wannan jiha bai zarce mutane dubu 800 ba, amma sakamakon zaben yana mai yin nuni ne a game da halin da ake ciki a kasar Jamus baki daya. Ita dai CDU tana cin gajiyar bacin rai dake tattare a zukatan mutane ne dangane da manufofin garambawul na gwamnatin tarayya. To sai dai kuma duk da haka karin goyan bayan da CDU ta samu bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta da gagarumar nasarar da jam’iyyar ta samu a zaben da ya gabata. Kazalika ba ta cimma burinta na samun kashi 50% na kuri’un da aka kada ba. Bisa ga dukkan alamu dai a yanzu jama’a sun ankara ne da cewar ita kanta CDU tana ba da goyan baya ga manufofin garambawul a saboda haka nasarar da ta samu a zaben tana da dangantaka da gagarumin farin jinin da gwamnanta a jihar Saarland Peter Müller ke da shi a wannan yanki. Dangane da SPD kuwa ko shakka babu ta kwashi kashinta a hannu, inda tayi asarar kashi 14% na magoya bayanta idan an kwatanta da zaben da ya gabata duk kuwa da kokarin da reshen jam’iyyar a Saarland yayi na kakkabe kansa daga manufofin garambawul na gwamnatin tarayya. Amma daya matsalar da dan takarar SPD a jihar ta Saarland Heiko Maas ya fuskanta ita ce kin cika alkawarin ba shi goyan baya da tsofon gwamnan jihar Oskar Lafontaine yayi a yakinsa na neman zabe. Kiraye-kiraye da Lafontaine ya rika gabatarwa domin shugaban gwamnati Gerhard Schröder yayi murabus da kuma kusantar juna da ake samu tsakaninsa da wata jam’iyya mai ra’ayin gurguzu duk sun taimaka wajen shafa wa SPD kashin kaza. Ita kuwa jam’iyyar The Greens, babu wani mai zarginta a game da matakan na garambawul duk da cewar tana da hannu a mulkin hadin guiwa na tarayya. Wani abin da ya taimaka mata kuma shi ne karancin masu kada kuri’a da aka fuskanta a zaben na jihar Saarland a jiya lahadi, domin ta haka kananan jam’iyyu ke da ikon taka rawar gani a zabubbukan da aka saba gudanarwa a nan kasar. Wannan maganar ta shafi jam’iyyun the Greens da FDP, wacce ita ma ta tsallake rijiya da baya domin sake komawa majalisar jihar Saarland. Ainifin magoya bayanta na marhabin da manufofin garambawul na garambawul kuma a sakamakon haka suka samu wata kwarin guiwa ta hana kane-kanen wata jam’iyya daya wajen tafiyar da mulki. Amma abin fargaba shi ne kashi hudu cikin dari da jam’iyyar NPD mai ra’ayin kyamar baki ta samu. Ga alamu jam’iyyar ta samu wannan ci gaba ne sakamakon tofin Allah tsine da ake wa manufofin gwamnati na garambawul. Wannan korafi da ake yi ba kakkautawa shi ne ya share mata wata hanya ta samun farin jini tsakanin jama’a. Kuma ko da yake hakan baya ma’anar yaduwar akidar kyamar baki amma tilas ne a sa ido akan wannan ci gaba.