Sakamakon zabe a Nigeria | Labarai | DW | 22.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zabe a Nigeria

A Nigeria ana cigaba da kidayar kuriú bayan zaben da aka kammala na shugaban kasa, sai dai jamaá na zaman zulumi sakamakon tarzoma da rashin tsari da suka dabaidabaye harkokin zaben. Masu sa ido na kungiyar tarayyar Turai sun baiyana matukar damuwa da yadda zaben ya gudana. A waje guda kuma sojoji sun bindige wasu matasa uku a garin Daura mahaifar dan takarar jamiýar adawa Muhammadu Buhari yayin da wasu gungun masu zanga zanga suka yi bore bayan samun rahotanni na bacewar wasu akwatunan zabe. Madugun jamíyar adawar Muhammadu Buhari yace babu wanda zai yi ikrarin samun nasarar lashe zaben a yanayi na magudi da almundahana, yana mai cewa ba zai bukaci magoya bayan sa su yi wata zanga zanga ba idan aka baiyana cewa jamíyar PDP ce ta lashe zaben. Shi ma dai mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar kuma dan takarar adawa wanda aka sanya sunan sa bisa umarnin kotu a cikin jerin yan takara dake neman kujerar shugabancin kasar ya baiyana zaben da cewa abin bakin ciki ne ga kasar baki daya. Ana sa ran zaben zai fidda wanda zai gaji shugaba mai barin gado Olusegun Obasanjo wanda jamíyar sa ta PDP ta tsaida Alhaji Umaru Musa Yar Adduá.