Sakamakon zabe a East Timor | Labarai | DW | 06.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zabe a East Timor

Bisa dukkan alamu Gwarzon fafutukan neman yanci a East Timor Xanana Gusmao na shirin kafa gwamnati,sakamakon sanarwar hadaka da wasu jammiiyu da jamiiyyarsa tayi.Hadin Gwiwar jammiyyar Gusmao da wasu kananan jamiiyyu masu sassaucin raayi guda biyu ,ya basu nasarar samun kashi 51 daga cikin 100 na adadin kuriu da aka kada a zaben yan majalisa daya gudana akarshen makon daya gabata a wanna kasa.Sai dai kuma ana iya kalubalantar wannan zabe a kotu.Tsohuwar jammiyyar dake mulkin kasar watau Fretilin,ta bayyana cewa bata amince da kasancewa yar adawa ba.Jammiyyar ce ta lashe mafi yawan kuriu,koda yake yawan kuriun bai isa bata daman jagorancin gwamnati.