Sakamakon zaɓen yan maljalisun dokoki a Turkiyya | Labarai | DW | 23.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zaɓen yan maljalisun dokoki a Turkiyya

Jam´iyar AKP ta praminista Tayeb Recep Erdowan na Turiyya ,ta samu gagaramin rinjaye a zaɓenyan majalisun dokoki da aka shirya jiya a fadin ƙasar baki ɗaya.

A sakamakon wannan zaɓe jam´iyar AKP, ta samu ƙarin kujeru 13 idan aka kwatanta da majalisar da ta gabata.

Wani baban abunda ya ɗauki hankali jama´a agame da wannan sakamako shine zaɓen yan majalisu ƙurdawa kussan 20, a sabuwar majalisar, wanda shine karo na farko, a tarihin demokradiyar Turkiyya.

Jimkadanbnayyanabayyana sakamakonna wucingadi Praminista Erdowan ya yi jawabi gaban ɗimbin magoya bayan sa:

„Wanda ya ci nasara wannan zaɓe ba jama´iyar AKP ba ce, a´a; Turkawa gaba ɗaya su ka yi nasara, da kuma makomar siyasa da haɗin kann ƙasar mu.

A yanzu za mu dukkufa wajen cimma bururukan da mu ka sa gaba, wanda su ka haɗa da ci gaba da tantanawa da ƙungiyar Eu, a game da shigar da Turkiya a matsayin memba.

Kazalika, za mu duƙufa wajen tabbatar da demokraɗiya cikin ƙasa“.

Ta ɓangare tattalin arziki, Praminista Erdogan ya alƙawarta gudanar da kwaskwarima, da zumar jera Turkiyya. Kafaɗa da kafaɗa da makwatan ta, na na nahiyar turai.