Sakamakon zaɓen ′yan Majalisa a Afghanistan | Siyasa | DW | 20.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakamakon zaɓen 'yan Majalisa a Afghanistan

Zaɓen na ranar Asabar ya fuskancin tashe tashen hankula

default

Zaɓen 'yan majalisar wakilai da ya gudana a ƙasar Afganistan,  ya fuskanci rigingimu da ya jagoranci kashe mutane 20, baya ga wasu 50 da suka jikkata. Ana saran samun sakamakon zaben nedai a watan Oktoba mai kamawa.

Ziaullah wani matashi ne ɗan shekaru 22 da haihuwa, yana ɗaya daga cikin mazauna babban birnin ƙasar na Kabul daya fito domin kaɗa ƙuri'arsa....

" bana jin tsoro, mutanen kabul basa jin tsaro. Akwai kyakkyawan tsaro a nan"

Ziaullah dai ya kasance na daga cikin mutanen Afghanistan da ke ganin cewar kawo yanzu ƙasarsa na bukatar gyara musamman ma ta fannin tsaro.

"Har yanzu muna bukatar tsaro, Kazalika akwai buƙatar bunkasa tattalin arzikinmu"

Afghanistan Leichen Mediziner Kabul

Tuni dai 'yan Taliban suka lashi takobin ganin cewar zaɓen 'yan majalisar ya fuskanci matsaloli, sai dai duk da wannan barazana da suka yi al'ummomin ƙasar ta Afghanistan  wajen kashi 40 daga ciki 100 sun fita domin kaɗa kuri'unsu, adadin da ƙasashen Duniya suka yaba. Fazel Alhmed Manawi shine shugaban hukumar Zaɓen ƙasar...

" akwai saɓani daga irin rahotanni da muke samu, sai dai akwai tabbacin cewar fararen hula 21 suka rasa rayukansu akan hanyarsu ta zuwa kada kuri'u, ayayinda wasu 46 suka samu raunuka. Kazalika akwai mutanen da aka sace"

Baya ga barazanar ta 'yan Taliban dai, wata babbar matsala da zaɓen ya fuskanta shine aran gizon kuri'u, inda aka samu rahotannin zaɓe fiye da sau guda, da cike akwatunan zaɓe da jabun ƙuri'u. Ana dai danganta irin arangizon kuri'u da aka fuskanta a zaɓen shugaban ƙasa na 2009 da yin tasiri akan rashin fitowar al'ummar ta Afghanistan domin  kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen na ranar Asabar data gabata.

To sai dai Commandan rundunar ƙasa da ƙasa dake ayyukan kiyaye zaman lafiya a Afghanistan  ta ISAF,  David Petreaus, ya yabawa irin rawa da jami'an tsaron cikin gida na Afghanistan suka taka tare da tallafin na ketaren a

"Mun kwashe shekarar da ta gabata wajen kokarin daidaita lamura a Afghanistan, kama daga tsarin yadda sojoji da jami'an tsaro zasu karɓi tafiyar da harkokin tsaro, da samar da shugabannin da suka dace tare da amfani da albarkatu da suka dace kamar tsaro , sintiri da uwa uba albarkatun kuɗi"

Hamid Karzai

A kwai bukatar gwamnatocin ƙasashen  yammaci su yi haɗin gwiwa da Afghanistan wajen ganin cewar sakamakon  wannan zaɓen 'yan majalisa da aka yi ya kasance mai tasiri wajen wajen inganta cigaban ƙasar akalla  a siyasance.

 To sai dai a yanzu haka dai masu lura da lamura da kaje su zo na cigaba da kira ga gwamnatin shugaba Hamid Karzai data bar hukuma mai zaman kanta ta binciki rahotannin arangizon ƙuri'u da ake zargin tabkawa a zaɓen 'yan majalisar wakilai daya gudana ranar Asabar. Masu sanya idanu kimanin 7,000 ne dai suka kasance a Afghanistan lokacin zaɓen, waɗan da suka ce akwai bukatar gudanar da bincike dangane da irin maguɗi da aka tabka.

A yanzu haka dai shugaba Hamida karzai ya soke halartar taron Majalisar Ɗunkin Duniya da  aka kaddamar a yau, domin cigaba da lura da sakamakon zaɓen da rigingimun cin hanci da maguɗi da suka mamaye shi.

Mawallafiya: Zainab Mohammad Abubakar

Edita          : Yahouza Sadissu Madobi